logo

HAUSA

An kira taron karawa juna sani kan ra’ayin yin mu’amala da koyi da juna game da wayewar kai a hedkwatar UNESCO

2024-04-16 09:50:03 CMG Hausa

Jiya Litinin, an kira taron karawa juna sani kan ra’ayin yin mu’amala da koyi da juna game da wayewar kai a hedkwatar hukumar kyautata ilmi, kimiyya da al’adu ta MDD wato UNESCO dake birnin Paris, fadar mulkin kasar Faransa. Masana daga kasar Sin da ma sauran kasashen duniya sun yi tattaunawa mai zurfi bisa taken “Yin mu’amala da koyi da juna game da wayewar kan bil Adama, da fatan dukkanin bil Adama na bai daya”.

An kaddamar da taron bisa hadin gwiwar ofishin labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, da hukumar UNESCO, da kuma kwamitin UNESCO na kasar Sin. A yayin bikin bude taron, mataimakin babban magatakardan hukumar UNESCO Qu Xing, da kuma mataimakin shugaban sashen fadakar da jama’a na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin Zhang Jianchun, sun ba da jawabai.

Qu Xing ya ce, idan babu fahimtar juna, da sanin juna, da amincewar juna, ba za mu iya samar da dunkulewar gamayyar kasa da kasa ba, ya kamata bangarori daban daban su kyautata fahimtar juna a tsakaninsu, domin bude sabon babi na zaman lafiyar duniya.

A nasa bangare kuma, Zhang Jianchun ya bayyana cewa, kasar Sin na aiwatar da ra’ayin yin mu’amala da koyi da juna game da wayewar kan al’umma, tana yin hadin gwiwa da sassa daban daban da abin ya shafa, ciki har da hukumar UNESCO, inda suka cimma sakamako da dama a fannin inganta mu’amalar wayewar kai a tsakanin bangarori daban daban.

Mahalarta taron sama da 200 da suka hada da jami’an hukumar UNESCO da wakilan kasashen mambobin MDD, da wakilan kungiyoyin kasa da kasa, da masanan kasashen duniya, da wakilan matasa daga kasashe da yankuna sama da 40 sun halarci taro na wannan karo. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)