logo

HAUSA

Yaki da ta’addanci: jami’an tsaro na FDS na Nijar sun farautar Boko Haram, wasu daga cikinsu sun mika wuya ga hukumomi

2024-04-16 10:01:57 CMG Hausa

’Yan makwannin baya bayan nan, a yankin Diffa an samun jerin mayakan kungiyar Boko Haram dake mika wuyansu ga jami’an tsaro na FDS dake ci gaba da farautar shugabanninsu a yankin tafkin Cadi.

Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Mayakan Boko Haram gomai suka yi saranda dalilin matsin lambar rundunar sojojin kasar Nijar, sun kai kansu ga hukumomin Bosso.

Haka ma a makon da ya gabata, wasu mayakan kungiyar Boko Haram da cibiyarta ke Najeriya, cikin dajin Sambissa suka ba da kansu ga jami’an tsaro na FDS dake Baroua, Toumour da kuma Bosso.

Matsin lamba dai na kara tsananta kan mayakan Boko Haram dake janyo tashe-tashen hankali a bangaren kudu maso gabashin Nijar tun yau da ’yan shekaru. A yau, farautar wadannan ’yan ta’adda na gudana a kai a kai, tare da kai samame ta jiragen saman yaki. Wannan rike wuta na sojojin Nijar na kara janyo rarrabuwar kawuna tsakanin kungiyar Boko Haram, abin dake janyo rikici tsakaninsu a cikin tsibirai na tafkin Cadi. Bayanan rundunar sojojin Nijar sun rawaito manyan gumurzu uku tsakaninsu na baya bayan nan daga cikin biyu a Najeriya kana guda a Cadi a ranar 27 ga watan Maris din shekarar 2024.

Wasu mayakan Boko Haram biyu ’yan asalin Cadi sun bada wuyansu a ranar 1 da ranar 2 watan Afrilu ga jami’an tsaro na FDS na Toumour bayan wani kazamin fada da ya hada gungun ISWAP da bangaren Bakoura dake arewaci. Lamarin da ya janyo fiye da mutuwar ’yan Boko Haram sama da dari da kashe karin wasu daga cikinsu.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.