logo

HAUSA

Kwamitin sulhu na MDD ya kira taron gaggawa kan rikicin Isra’ila da Iran

2024-04-15 11:43:47 CMG Hausa

Jiya Lahadi, kwamitin sulhu na MDD ya kira wani taron gaggawa bisa bukatun Isra’ila, kan matakin soja da Iran ta dauka a kanta.

Mukaddashin wakilin dindindin na kasar Sin dake majalisar Dai Bing ya bayyana cewa, Sin ta yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su yi iya kokarinsu su kai zuciya nesa, kuma su yi la’akari da ra’ayoyin bangarori daban daban wajen magance rikicin bisa kundin tsarin mulkin majalisar da dokar kasa da kasa, ta yadda za a kauracewa tsanantar da halin da ake ciki.

Shugaban kasar Iran Seyed Ebrahim Raisi ya ba da wata sanarwa a wannan rana cewa, sojin Iran na sa ido kan halin da ake ciki a yankin, da duk wani matakin da za a dauka wanda zai keta muradun Iran, kuma za ta mayar da martani mai tsanani.

Ban da wannan kuma, minsitan tsaron kasar Amurka Lloyd Austin ya hira da takwaransa na Isra’ila Yoav Gallant ta wayar tarho a wannan rana, inda ya nanata cewa, Amurka ba ta son tada rikici da Iran, amma za ta ci gaba da daukar matakan da suka wajaba don tabbatar da tsaron jama’ar Isra’ila da Amurka.

An kuma labarta cewa, shugabannin kungiyar G7 sun yi taro ta kafar bidiyo a wannan rana, inda suka tattauna kan martanin diplomasiyya da za a mayar kan lamarin, kuma an yi kira ga bangarorin da lamarin ya shafa da su yi hakuri da juna da daukar matakan da suka dace don kwantar da hankali. (Amina Xu)