logo

HAUSA

Amurka: Mai Shafawa Sauran Kasashe Bakin Fenti

2024-04-15 09:49:18 CMG Hausa

 

DAGA MINA

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony J. Blinken, a gun “taron kolin Demokuradiyya” da aka gudanar a kwanan baya, ya zargi kasar Sin da gurbata yanayin sadarwa, da yada labarai na jabu. Amma ko hakan gaskiya ne? Alal hakika, wane ne ke yada labaran jabu?

Kowa ya san cewa Amurka kasa ce da ta fi yada labarai na jabu da kirkirarsu. Tun lokacin cacar baka, Amurka ta rika sayen kafofin yada labarai karkashin wani shiri mai suna “Operation Mockingbird” don su yi abin da take so.

A shekarun baya-baya nan, ganin yadda Sin ta bunkasa cikin sauri, Amurka ta mai da ita abokiyar takara mafi girma, har ma ta tada yakin bayanai a kanta. Kwanan baya, wani masanin Turai mai suna Jan Oberg ya fayyace cewa, a shekarun baya, majalisar dokokin kasar Amurka ta zartas da wani kudiri na ware kudi har dallar Amurka biliyan 1.5, don horas da‘yan jaridar kasashen yamma cikin tsawon shekaru 5, don su rubuta labaran shafawa kasar Sin bakin fenti. Kaza lika, ba sau daya ba, ‘yan siyasar Amurka ciki har da shugaban hukumar leken asiri ta CIA sun amince cewa, Amurka ta dauki wasu matakai a boye, ciki har da sayen wasu kafofin yada labarai don shafawa kasar Sin bakin fenti, abin da ya shaida cewa, Amurka ta tsai da shirin shafawa Sin bakin fenti cikin dogon lokaci.

Yanzu Sin na samun bunkasuwar tattalin arziki mai karko, amma Amurka ta yada labarai wai tattalin arzikin kasar Sin zai dakushe. A yayin da shawarar “ziri daya da hanya daya” ke amfanar al’ummar kasashe daban-daban, Amurka ta ce wai tarkon bashi ne. A yayin da al’ummar kasashe da dama ke bayyana hakikanin abin da suka ji ko gani a Sin, Amurka ta ce wai Sin ta sayi kafafen yada labarai. Ban da wannan kuma, Amurka ta bayyana matakan da Sin take dauka na bunkasa tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al’umma a jihar Xinjiang a matsayin aikin tilas da kisan kare dangi. Shin ko Amurka ta fadi gaskiya? Gwano ba ya jin warin jikinsa.

Hausawa kan ce “Munafuncin dodo ya kan ci mai shi”. Amurka tana yunkurin gurbata gaskiya, amma duk da haka sauran kasashe na fahimtar burinta sosai, kuma ba za a amince da hakan ba ko kadan. (Mai zane da rubutu: MINA)