logo

HAUSA

Kafar yada labarai ta Amurka: Basussukan Amurka ne abokin gabanta mafi girma

2024-04-15 11:45:38 CMG Hausa

Shafin yanar gizo na muradun Amurka ya ba da wani rahoto kwanan baya cewa, yawan basussukan da ke kan gwamnatin Amurka ya kai kimanin dala triliyan 35, wanda ya kasance abokin gaba mafi girma da Amurka ke fuskanta.

Rahoton ya nuna cewa, tun bayan babban yakin duniya na daya, Amurka ta tabbatar da fifikon matsayinta a fannin tattalin arziki, hakan ya sa kudinta na dala ya zama kudin da dole ko wace kasa ta mallake shi.

Ban da wannan kuma, rahoton ya ce, a ganin wasu ‘yan siyasar Amurka, gibin kasafin kudi ba matsala ba ce, wai idan Amurka ta dade tana kan wannan matsayi na samun fifiko a duniya, to za ta iya kashe kudi yadda ta ga dama. Sai dai, tattalin arzikin kasar na fuskantar matsi matuka, ganin yadda gwamnatin kasar karkashin Donald Trump da Joe Biden sun haifar da gibin kasafin kudi mafi tsanani, lamarin da ya haddasa saurin hauhawar farashin kayayyakin masarufi da kudin ruwa na bankuna, lamarin da ya yi mummunar tasiri ga rayuwar fararen hular kasar matuka.

Kazalika, rahoton ya ce, sauran kasashe a duniya musamman ma kasashe masu tasowa, ba su da kwarin gwiwa kan makomar tattalin arzikin Amurka, a sa’i daya kuma, wadannan kasashe suna damuwa matuka kan matakin mayar da kudin dala makami da Amurka take yi, wanda ke musu babbar barazana. Hakan ya sa, wadannan kasashe ke daidaita manufarsu don magance matsala. Sai dai tsarin hada-hadar kudi na kasar Amurka zai tabarbare, idan aka maye gurbin dala a matsayin babban kudin da ake ajiyewa a duniya, kamar yadda aka rubuta a cikin rahoton.(Amina Xu)