logo

HAUSA

Amurka Mai Matukar Son Kutse Ta Yanar Gizo Ta Zargi Wasu Kan Wannan Batu

2024-04-15 09:49:45 CMG Hausa

DAGA MINA

Kwanan baya, gwamnatocin Amurka da Birtaniya sun zargi kasar Sin da cewa, wai wata kungiya mai kutse ta yanar gizo dake da alaka da gwamnatin kasar ta yi kutse ta yanar gizo kan wadannan kasashen biyu. Abin dariya ne, mai sarautar kutse ta yanar gizo na zargi wasu da aikata hakan, gwano ba ya jin warin jikinsa.

Kowa ya sani, Amurka ta fi yin kutse ta yanar gizo, kuma ta zama babbar barazana ga duniya kan yanar gizo. Kasar ta dade tana amfani da fifikonta a fannin kimiyyar sadarwa da albarkatun yanar gizo na kungiyar leken aisiri ta FVEY(Five Eyes Alliance), don leken asirin sauran kasashe ciki har da kawayenta, da satar bayanan shugabanni da kamfanoni har da fararen hula na kasashen. Ko a cikin farkon watanni uku na bana, Amurka ta yi kutse kan yanar gizo na wasu kasashe har fiye da sau 2000, ciki hadda kasar Sin, kuma ta yi hakan ne daga babban yankinta ko sansanonin sojinta a ketare.

Gwamnatocin Amurka da Birtaniya sun saba da yin kutse ta yanar gizon sauran kasashe, amma a wani bangare na daban, sun kirkiro labarin bogi don shafawa kasar Sin bakin fenti a wannan bangare. Laifi tudu ne, ka taka naka ka hango na wasu, wadannan kasashe sun siyasantar da wannan batu, don hana bunkasuwar kasar Sin.

Tsaron yanar gizo kalubale ne da ko wace kasa ke fuskanta, kuma kare tsaron yanar gizon nauyi ne da ya rataya a wuyan dukkan al’ummomin duniya. Sin na tsayawa tsayin daka kan yin amfani da yanar gizo yadda ya kamata, kuma ta ki amincewa da siyasantar da batun tsaron yanar gizo, haka kuma tana kokarin dakile duk wani nau’in kutse kan yanar gizo. (Mai zane da rubutu: MINA)