logo

HAUSA

CICPE Na 2024 Dama Ce Ga Kasashen Ketare Ta Fahimtar Kasuwar Sin

2024-04-15 17:04:39 CMG Hausa

Baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa na kasar Sin karo na 4 ko CICPE a takaice, wanda aka fara daga ran 13 ga wannan watan a Haikou, babban birnin lardin Hainan, shi ne baje kolin kasa da kasa na farko na kasar Sin na kayayyakin masarufi, kuma mafi girma a yankin Asiya da tekun Pasifik.

A matsayin baje kolin kasa da kasa na farko a kasar Sin a shekarar 2024, ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa harkokin cinikayya a tsakanin kasar Sin da sauran kasashe da kuma kara habaka shigo da kayayyaki masu inganci. Musamman ma, ya kasance wata kafa ga kamfanoni na kasa da kasa don samun damar shiga babbar kasuwar kayayyakin masarufi na kasar Sin wadda ta kasance daya daga cikin mafi girma da kuma saurin bunkasuwa a duniya, kuma babbar dama ga 'yan kasuwan duniya wajen tallata hajojinsu.

Baje kolin na bana ya zarce wanda aka gudanar a baya da girman fili mai fadin murabba'in mita 128,000, kuma ya hada kayayyakin masarufi masu inganci daga gida da waje, da masu saya da sayarwa daga duk fadin duniya, tare da  ba da gudummawa wajen fadada kasuwannin kayayyakin masarufi na kasar Sin, da kuma biyan bukatar kayayyaki na musamman kuma masu inganci.

Baje kolin ya bayyana karfin saya da sayarwa na jama'ar kasar Sin, domin ya gabatar da sabbin kayayyaki na zamani da ake bukata, da kayayyaki daban-daban na kasa da kasa ga mahalarta, da wadatar zabi ga masu sayayya bisa bukatunsu, da kuma bunkasa kasuwar kayayyakin masarufi a kasar Sin.

An zabi Ireland a matsayin babban bako na baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa na bana wanda ke gudana daga ranar 13 zuwa 18 ga watan Afrilu, yayin da Italiya, Faransa, Jamhuriyar Czech, Japan, Kanada da Switzerland suka kafa rumfunan a matsayin mahalarta na kasa da kasa. (Yahaya Mohammed)