logo

HAUSA

An gudanar da taron tunawa da ranar da ’yan kungiyar Boko Haram suka sace ’yan matan Chibok 276 a jihar Borno

2024-04-15 09:49:26 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya ta sha alwashin ceto raguwar ’yan matan makarantar Chibok da suka yi saura a hannun ’yan kungiyar Boko Haram.

Kwamashinan yada labarai da harkokin tsaron cikin gida na jihar Borno Farfesa Usman Tar ne ya tabbatar da hakan yayin wani taron manema labarai a garin Maiduguri, inda ya ce, gwamnati ba za ta saurara ba har sai ta tabbatar daliban sun sadu da iyalan su.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

A ranar 14 ga watan Afirilun 2014, ’yan ta’addan kungiyar Boko Haram suka sace dalibai ’yan makarnatar sakandaren matan garin Chibok dake kudu maso gabashin Maiduguri har su 276.

Kwamshinan yada labaran na jihar Borno ya ce, gwamnati da al’ummar jihar ba za su taba mantawa da abun da ya faru ga wadannan ’yan mata ba shekaru 10 da suka gabata, lamarin da ya shafe tasirin karatun ’ya’ya mata a jihar .

Ya ce, ana samun ci gaba sosai a aikin hadin gwiwar da ake yi tsakanin gwamnatin jihar ta Borno da gwamnatin tarayyar wajen tabbatar da ganin daliban da suka yi raguwa a hannun ’yan Bokon Haram din sun dawo cikin iyalansu, wanda yanzu haka dalibai 187 ne aka samu cetowa daga cikin su dari 276.

“A wannan rana ta juyayin cika shekaru 10 da sace ’yan matan na Chibok, gwamnatin jihar Borno tana kara mika sakonnin jajenta ga iyayen wadannan dalibai, haka kuma gwamnati na kara tabbatar wa jama’a cewa za ta ci gaba da taya iyayen yaran da har yanzu ’ya’yansu ke a tsare a hannun ’yan Boko Haram alhinin wannan munmunan abun da ya faru.”

Kwamshinan yada labaru na jihar Borno haka kuma ya sanar da cewa, ’yan matan na Chibok 16 da aka ceto kwanan nan suna karkashin kulawar gwmnatin jihar ne inda ake ba su horon koyon sana’o’i, yayin da kuma ’ya’yan da suka haifa an sanya su a makarantun renon yara. Koda yake 4 daga cikin daliban sun yanke shawarar komawa ga iyayensu domin ci gaba da rayuwa. (Garba Abdullahi Bagwai)