logo

HAUSA

Liang Jianying ta jagoranci tawagarta don taimakawa aikin gina layin dogo na kasar Sin wajen samun saurin ci gaba

2024-04-15 16:32:21 CMG Hausa

Liang Jianying tana da alaka da jiragen kasa tun tana karama, kuma ta zama mai tsara layin dogo bayan kammala karatunta a jami'a. Ta jagoranci tawagarta wajen samun manyan fasahohin zamani, da samar da nau’ikan jiragen kasa masu sauri daban-daban, tare da taimakawa aikin gina layin dogo na kasar Sin wajen samun ci gaba cikin sauri. Har ma ta lashe lambar yabo ta "Injiniya ta kasa" a kasar Sin, kuma ta zama jarumar da ta cancanci yabo a fannin aikin gina layin dogo.

To, wane irin hali ne take da shi? Wadanne labarai ne suka faru a kanta? Kuma wane dalili ne ya zaburar da ita don cimma burinta? A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku labari ne game da wannan baiwar Allah, mai suna Liang Jianying.

A shekarar 1972, an haifi Liang Jianying a cikin wani iyali na talakawa a lardin Jilin da ke arewa maso gabashin kasar Sin, tun bayan haihuwarta, tana da alaka da jiragen kasa.

Mahaifin Liang Jianying ma'aikaci ne dake aiki a harkar layin dogo, kuma gidanta yana da nisan kimanin mil dari uku kacal daga tashar jirgin kasa. Tun tana karama, Liang Jianying tana son zama a gaban taga, tana kallon jiragen kasa dake wuce a gabanta.

A shekarar 1991, bayan kammala karatun sakandare, Liang Jianying ta samu nasarar shiga jami'ar da take so, wato Jami’ar Koyon Ilmin Layukan Dogo ta Shanghai.

Daga garinsu na lardin Jilin dake arewa maso gabashin kasar Sin zuwa birnin Shanghai dake gabashin kasar, daga karshe Liang Jianying ta samu damar hawa jirgin kasa. Amma sai a wannan lokacin ne ta ji tazara tsakanin tunaninta da kuma zahiri game da jiragen kasa. Liang Jianying ta dauki jirgin kasa daga Jilin zuwa Shanghai ita kadai, duk da haka, wannan tafiya ba ta yi mata dadi ba.

Liang Jianying ta gano cewa, ba kawai sararin da ke cikin jirgin kasa ba shi da fa’ida kamar yadda take zato ba, har ma yawo a cikin jirgin yana da matukar wahala. Domin adana kudi, mutane da yawa suna sayen tikitin dakin tsayawa, wanda kuma ya sa wurin da asali dan karami ne ya kasance mafi cunkoso. Bugu da kari, saboda rashin ci gaban tsarin sufuri a wancan lokacin, Liang Jianying ta kan bukaci sauya jiragen kasa daga Jilin zuwa Shanghai, wanda ta kan yi amfani da sa'o'i kusan 50.

Daga nan ne Liang Jianying ta fara fuskantar tafiya a jirgin kasa a zagaye biyu a duk lokacin sanyi da bazara a ko wace shekara, kowannensu zai kai kusan tsawon kwana biyu da dare biyu. Wannan tafiya cikin mawuyacin hali a ko da yaushe ya sanya Liang Jianying jin radadi matuka a lokacin da take karatu a jami’a. Kuma ganin wahalar da fuskanta, ta kudiri aniyar raya harkokin sufuri na kasar ta Sin a nan gaba.       

A shekarar 1995, Liang Jianying ta kammala karatunta a jami’a, kuma ta samu damar shiga kamfanin Sifang, wato reshen kamfanin CRRC na kasar Sin dake birnin Qingdao na kasar, don kama aikin tsara jiragen kasa, inda kuma ta fara kama hanyar neman cimma burinta bisa ga manufar sanya jiragen kasa su kasance masu walwala, da sauri, da baiwa fasinjoji karin kwanciyar hankali.

Shekara ta 2004, shekara ce ta farko da aka fara raya harkokin jiragen kasa masu saurin tafiya a kasar Sin. Shirin da kasar ta fitar game da "Tsarin layin dogo na matsakaici da na dogon lokaci", ya bude sabon shafi ga saurin bunkasuwar layin dogo na kasar ta Sin. A sa'i daya kuma, ya zaburar da "mafarkin gini" na Liang Jianying a cikin zuciyarta.

Dukkan ma'aikatan fasaha sun yi matukar farin ciki da haka, a ganinsu, wannan na bayyana cewa, kasarsu da jama'ar kasar sun sanya fatansu na raya harkokin sufuri a kansu. Amma bayan jin dadi, sun kuma ji matsi da ba a taba gani ba.

Liang Jianying ta bayyana cewa, bunkasuwar jiragen kasa masu saurin tafiya na kasar Sin ya biyo bayan hanyar shigowa, da nazari, da koyo, da kuma kara yin kirkire-kirkire a kai.

Amma abokan hulda na kasashen waje za su sanar da yadda za su gudanar da kowane mataki, ba tare da ambaton tsarin fidda jigon jiragen kasa ba. Ta hakan, Liang Jianying ta fahimci sosai cewa, ana iya sayen kayayyaki daga kasashen waje, amma ba za a iya sayen kwarewar yin kirkire-kirkire kan fasahohi ba.

A shekarar 2006, kamfanin Sifang ya fara nazari da kera jirgin kasa mai saurin tafiya, wanda ke gudu da saurin kilomita 300 a cikin sa'a guda. Liang Jianying ta yi aiki a matsayin babban mai tsare-tsare kan wannan aiki, kuma wannan ne karo na farko da ta tsara jirgin kasa mai saurin tafiya da kanta. 

Kera jiragen kasa masu saurin tafiya, wani babban aiki ne mai cikkken tsari, jirgin kasa mai saurin tafiya guda daya na hade da sassan inji sama da dubu 500. Bayan karuwar gudun daga kilomita 200 a cikin sa'a 1 zuwa kilomita 300 a cikin sa'a 1, akwai wasu shingaye masu wuyar gaske da dama a bangaren fasaha, wadanda ke bukatar a kawar da su.

Daga ayyukan binciken muhimman fasahohi zuwa na tsara shirye-shirye, daga ayyukan nazarin kwaikwayon hakikanin hali zuwa na tabbatarwa ta hanyar yin gwaji, Liang Jianying ta jagoranci tawagarta  wajen shawo kan matsalolin da ake fuskanta ta fuskar fasaha daya bayan daya.

Liang Jianying ta tuna da cewa, a lokacin, ba ta ma samun lokacin kula da karamar 'yarta, a kowace rana idan ta dawo gida daga aiki, 'yarta ta riga ta yi barci, kuma idan ta fita zuwa dakin tsare-tsare da safe, 'yarta ba ta farka ba. Wata rana 'yarta ta buga mata waya cewa, "Mama, ina so ki ci abinci tare da ni." Liang Jianying ta ji bakin ciki sosai a cikin zuciyarta, amma duk da haka, ba ta iya cika burin 'yarta ba.

A watan Disamba na shekarar 2007, tawagar Liang Jianying ta yi nasarar samun ci gaba a fannin fasahar karfin iska da wasu muhimman fasahohi da dama, ta hakan kuma aka samar da jirgin kasa na farko mai gudun kilomita 350 a cikin sa'a guda a kasar Sin.

To, masu sauraro, iyakacin shirinmu na yau ke nan, amma ba za mu dasa aya kan labarin Liang Jianying, wadda ta jagoranci tawagarta wajen samar da nau’ikan jiragen kasa masu sauri daban-daban, tare da taimakawa aikin gina layin dogo na kasar Sin wajen samun ci gaba cikin sauri, a mako mai zuwa, za mu ci gaba da kawo muku labari kan wannan baiwar Allah.