logo

HAUSA

An kulla Yarjejeniyar hadin gwiwar danyen mai a tsakanin Sin da Nijer

2024-04-15 10:37:33 CMG Hausa

A ranar 12 ga wata, firaministan kasar Nijer Lamine Zeine Ali Mahaman da wakilin kamfanin kasar Sin mai kula da aikin haka da sarrafa danyen mai na CNPC, sun kulla jerin yarjeniyoyin hadin gwiwa a fannin danyen mai, inda jakadan kasar Sin dake kasar Nijer Jiang Feng ya kuma halarci bikin kulla yarjeniyoyin, tare da wasu mambobin majalisar ministocin kasar Nijer.

A yayin bikin, Lamine Zeine ya yi jawabi cewa, yanzu kasar Nijer na cikin wani muhimmin mataki a kokarinta na fitar da danyen mai zuwa kasashen waje. Kana yarjeniyoyin da aka kulla sun nuna cewa, an bude sabon babin hadin gwiwar Sin da Nijer, ta fuskar haka da sarrafa danyen mai. Ya kuma nuna yabo kan zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa, kasar Sin babbar abokiyar kasar Nijer ce.

A yayin da yake zantawa da wakilan Babban Gidan Talabijin na Kasar Nijer da ma sauran kafofin watsa labarai na kasar, jakadan kasar Sin Jiang Feng ya bayyana cewa, yarjeniyoyin da aka kulla sun nuna cewa, an cimma sabbin sakamako bisa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Nijer a fannin raya harkoki masu alaka da danyen mai. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)