logo

HAUSA

Iran ta kaddamar da hare hare kan Isra’ila wanda ta ce na ramuwar gayya ne

2024-04-14 12:13:00 CMG Hausa

A daren jiya Asabar, rundunar juyin juya halin Islama ta kasar Iran (Iran's Islamic Revolutionary Guard Corps), ta tabbatar da cewa, kasar ta fara kaddamar da hare haren jirage marasa matuka, da makamai masu linzami kan Isra’ila, a wani mataki da Iran din ta ce na ramuwar gayya ne.

Rahotanni na cewa a jiya Asabar, Amurka da kawayen ta sun kakkabo wani adadi na jirage marasa matuka da Iran ta harba zuwa yankunan Isra’ila.

Yanzu haka dai kasashe da dama na gabas ta tsakiya cikin har da Jordan, Lebanon da Iraqi, sun dakatar da zirga zirgar jiragen sama ta samaniyar yankunan su.

Jim kadan kafin bullar labarin hare haren na Iran, firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, sun girke tsarin kandagarkin makamai domin jiran ko wane irin yanayi na ko ta kwana.

An jiyo kara mai tsanani ta ababen fashewa a birnin Kudus, wadda kafafen watsa labarai na Isra’ila suka ce ta makaman da Iran ta harba ne da aka kakkabo.

Ofishin wakilcin kasar Iran a MDD ya ce harin ramuwar gayya ne ga harin da Isra’ila ta kai cikin harabar ofishin jakadancin ta dake Damascus a ranar 1 ga watan nan na Afirilu, wanda ya hallaka wasu dakarun juyin juya halin Islama na Iran din su 7, ciki har da manyan kwamandoji 2.

Cikin sakon da ya wallafa ta shafinsa na X, ofishin ya ce idan Isra’ila ta sake yin wani kuskuren, martanin Iran zai kara tsananta. Kaza lika ya gargadi Amurka da ta kaucewa tsoma hannu cikin lamarin, kasancewarsa rikici ne tsakanın Iran da Isra’ila.

To sai dai kuma shugaban Amurka Joe Biden, wanda a ranar Juma’a ya gargadi Iran da kada ta kaiwa Isra’ila hari, duk da ya ce akwai yiwuwar hakan, ya yi alkawarin goyon bayan Isra’ila kan Iran, kamar dai yadda fadar White House ta bayyana.