logo

HAUSA

Fadar shugaban tarayyar Najeriya ta nemi hadin kan gwamnoni da shugabancin majalissa domin ciyar da Kasa gaba

2024-04-14 16:28:05 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi kiran kara samun hadin kai mai karfi tsakanin gwamnatin tarayyar da gwamnonin jahohi da kuma `yan majalissar dokokin kasar domin cimma burin muradun cigaban kasa.

Shugaban ya yi wannan kiran ne a gidan sa da ke birnin Legos, lokacin da yake karbar bakuncin gwamnonin jahohi da kuma shugabannin majalissun dokokin kasar yayin ziyarar barka da salla da suka kai masa, ya ce samun kyakkyawar alaka a tsakanin wadannan bangarori uku na Najeriya zata iya kaiwa ga wani babban matsayi a nan gaba kadan.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Shugaban na tarayyar Najeriya ya ce duk da dai akwai fahimtar juna tsakaninsa da ‘yan majalissar kasar da kuma daukacin gwamnonin jahohi, amma wannan ba za ta hana shi sake neman alfarmar su ba bisa irin muhimmancin da suke da shi wajen cimma manufar gwamnatinsa ta nemarwa kasar makoma tagari.

Tawagar gwamnonin da na `yan majalissar ta kasance ne karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima, inda a lokacin da yake jawabi ya shaidawa shugaban na Najeriya cewa sun ziyarce shi ne domin taya shi murnar sallah tare da kuma tabbatar masa cewa zai cigaba da samun hadin kai da goyon bayan su a ko da yaushe.

Mataimakin shugaban kasar ya cigaba da cewa lokaci ya wuce da shugabannin za su rinka barin banbancin addini da na kabilanci ya rinka yin tasiri a wajen jagorancinsu, inda ya ce ci gaba baya tabbatuwa a yanayin da kawunan al`umma ke a rarrabe.

Sanata Kashim Shettima ya yaba mutuka bisa samun halartar gwamnoni 27 wajen wannan ziyara duk kuwa da banbancin jam`iyyun dake tsakanin su.

Haka kuma mataimakin shugaban kasar ya bayyana farin cikin yadda tattalin arzikin Najeriya ke kara dawowa haiyacin sa bayan koma bayan da ya samu a `yan shekarun baya, yanzu abun da ake bukata shi ne hadin kan dukkan masu ruwa da tsaki.

“Mu hada kan mu, mu marawa shugabannin mu baya domin daga matsayin kasar nan zuwa wani mataki babba”

A jawabin sa shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazaq alkawari ya yi na cewa a shirye gwamnonin kasar suke su marawa duk wasu shirye shirye da manufofin raya kasa da shugaba Tinubu ya bijiro da su.(Garba Abdullahi Bagwai)