logo

HAUSA

Sakatare-janar na MDD ya yi kira ga Iran da Isra’ila da su dakatar da aiwatar da matakan nuna wa juna kiyayya

2024-04-14 16:27:47 CMG Hausa

Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya fitar da sanarwa ta hannun kakakinsa jiya Asabar, inda ya yi kira ga kasashen Iran da Isra’ila, su dakatar da aiwatar da matakan nuna wa juna kiyayya, tare da yin tir da tsanantar halin da ake ciki, ganin yadda Iran ta kaddamar da gagarumin hari kan Isra’ila. Guterres ya kuma jaddada cewa, wannan shiyya, da ma duniya baki daya ba za su jurewa barkewar wani sabon yaki ba.

Kaza lika, wasu kasashen Gabas ta Tsakiya da dama, ciki har da Saudiyya, da Qatar, da Jordan, sun fitar da sanarwa, inda suka yi kira ga bangarori daban-daban da su natsu, don kaucewa tabarbarewar yanayin da ake ciki.

Shugaban kasar Amurka Joe Biden, shi ma ya fitar da sanarwa a jiya Asabar, inda ya ce, kasarsa za ta kira taron shugabannin kasashen G7 a yau Lahadi, don tattaunawa kan matakan diflomasiyyar da za su dauka kan wannan abun. Biden ya ce, rundunar sojojin Amurka ta taimaki Isra’ila wajen kakkabo “kusan dukkan” jirage marasa matuka, da makamai masu linzami da Iran ta harba.

Bugu da kari, rahotanni daga kafafen yada labaran Isra’ila sun ce, yayin tattaunawar Biden da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ta wayar tarho, Biden ya ce Amurka ba za ta goyi bayan Isra’ila ta kaddamar da ramuwar gayya kan harin Iran ba, kana ba za ta shiga cikin rikicin ba. (Murtala Zhang)