logo

HAUSA

Zanga zanga tare da maci na ‘yan Nijar domin neman sojojin Amurka da su fice daga kasar Nijar

2024-04-14 16:35:34 CMG Hausa

Daruruwan ‘yan Nijar maza da mata, yaro da babba suka amsa kira kwamitin goyon bayan kwamitin ceton kasa na CNSP a ranar jiya Asabar 13 ga watan Afrilun shekarar 2024, inda suka fito dafifi a kan titunan birnin Yamai tun daga karfe takwas da rabi na safe har zuwa karfe 12 da rabi na rana. Bukatarsu ita ce na ganin sojojin Amurka sun fita daga Nijar.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Haduwar da ta fara daga dandalin Place Toumo  har zuwa dandalin maharabar majalisar dokokin kasa da aka fi sani da Place de la concertation, domin yin allawadai game da kasancewar sojojin kasar Amurka a Nijar, musammun ma a yankin Agadez da na Tillabery. Maganar tsaro ta fara lalacewa tsakanin kasashen biyu, tun lokacin da sabbin hukumomin soja na kasar Nijar suka soki tare da nuna damuwarsu kai tsaye kan yarjejeniyar tsaro da ta soja, da gwamnatin tsohon shugaban kasa, Issoufou Mahamdou ta sanyawa hannu tare da kasar Amurka a shekarar 2012. Wacce shugaban kasa, Mohamed Bazoum ya ci gaba da girmamawa kafin sojoji suka kwace masa mulki a ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023 a karkashin jagorancin birgadiye janar Abdourahamane Tiani.

Wannan al’amarin dai ya biyo bayan da Nijar ta tilastawa sojojin Faransa ficewa daga kasarta yau da watanni hudu da suka gabata.

Cikin wannan yanayi ne, masu zanga zangar suka yi tattaki har zuwa dandalin maharabar majalisar dokoki, yawancinsu rike da tutocin kasar Nijar da alluna masu rubuce-rubucen da ke bayyana fatan ‘yan Nijar na ganin sojojin Amurka sun fita daga Nijar.

Yayin da wasu masu zanga zangar suka nuna cewa kasancewar sojojin yammacin duniya a Nijar, shi ne dalilin ta’addanci da rashin tsaro da kasashen AES suke fuskanta, musamman kasar Nijar.

Kwamitin goyon bayan CNSP ya bayyana cewa, al’ummar Nijar ta amsa kiran kungiyoyin fararen hula da ke kishin kasa, inda suka rika cewa zancen kasa, sai ‘yan kasa, domin shaida wa duniya cewa ‘yan Nijar ba su bukatar zaman sojojin Amurka a Nijar.

Mohamed El Kebir daya daga cikin shugabannin wannan zanga zanga tare da maci, ya bayyana cewa ‘yan Nijar za su ci gaba da yin irin wadannan tarukan gangami a kai a kai har sai sun ga sojojin Amurka sun fita daga kasar Nijar baki daya.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.