logo

HAUSA

Shatile wasu ba ya karawa mai yin hakan saurin tafiya

2024-04-14 22:00:00 CMG Hausa

A ‘yan kwanakin nan, wasu kasashen yammacin duniya sun sha zargin kasar Sin da “samar da hajoji fiye da kima”, wadanda a cewarsu, wai kayayyakin da masana’antun kasar Sin suka samar, musamman ma motocin lantarki, da batirin Lithium, da farantan samar da lantarki ta hasken rana, wadanda “suke cika kasuwannin duniya cikin farashi mai matukar rahusa”, kuma “Yadda kasar Sin ke samar da hajoji fiye da kima ka iya haifar da barazana ga bunkasuwar masana’antun sauran kasashe, har da tattalin arzikin duniya.”

Amma a hakika, a zargin da suke yi wa kasar Sin, Amurka da kungiyar tarayyar Turai sun bayyana “samar da hajoji fiye da kima” a matsayin yadda ake samar da hajoji fiye da bukatun gida, wanda bai dace ba. Idan mun yi nazari, kaso 1/5 na amfanin gonar da manoman kasar Amurka suke samarwa ana fitar da su ne ga kasar Sin, kuma daga cikin motoci kimanin miliyan 4.1 da kamfanonin samar da motoci na kasar Jamus suka kera a bara, miliyan 3.1 ne aka fitar da su zuwa kasashen ketare. To, idan “samar da hajoji fiye da kima” na nufin yadda ake samar da hajoji fiye da bukatun gida, ko wadannan kasashe ma suna samar da hajojinsu fiye da kima? Idan kuma hakan ne, yaya za a yi da ciniki a tsakanin kasa da kasa? 

Ban da haka, bisa lissafin da hukumar kula da makamashi ta duniya ta yi, an ce, ya zuwa shekarar 2030, adadin motoci masu aiki da sabbin makamashi da ake bukata a fadin duniya zai kai miliyan 45, wanda ya ninka na shekarar 2022 har sau 4.5. Sa’an nan, yawan wutar lantarki da aka samar ta hasken rana da ake bukata za ta ninka na shekarar 2022 har sau 4. Ta hakan muna iya gano cewa, akwai babban gibi a tsakanin kayayyakin da ake samarwa da ma bukatun kasuwanni, musamman bukatar kasashe masu tasowa ta fannin kayayyaki masu aiki da sabbin makamashi. Abin da mutanen kasashen yamma suka fada na wai “kasar Sin na samar da kayayyaki fiye da kima”, sam ba gaskiya ba ne.

Motocin lantarki, da batirin Lithium, da farantan samar da lantarki ta hasken rana da kasar Sin ke samarwa, suna samun matukar karbuwa a kasuwannin duniya ne sabo da yadda kamfanonin kasar Sin suka dukufa a kan kirkire-kirkiren fasahohi, da kasuwar kasar mai matukar girma, da cikakken tsarin masana’antun kasar, da ma daidaiton da kasa da kasa suka cimma na tinkarar sauyin yanayi. Har ila yau, kayayyaki masu inganci na kasar Sin na biyan bukatun kasashen duniya, a sa’in da kasar ke ba da gudummawarta a kokarin da kasa da kasa ke yi na tinkarar sauyin yanayi.

A lokacin da ake kokarin tinkarar sauyin yanayin duniya, wasu mutanen kasashen yamma suna alakanta matsalar da ake fuskanta da karancin sabbin makamashin da aka samar, amma su ne suke zargin kasar Sin da samar da sabbin makamashi “fiye da kima”. Ta bangaren shige da fice na motoci kuma, yawan motocin lantarki da kasar Sin ta fitar zuwa Turai ya kai kaso 8% ne kawai na kasuwannin kasashen Turai, amma an ce kasar ta samar da motoci fiye da kima, a yayin da aka daukaka kasar Jamus a matsayin kasa mai karfi wajen samar da motoci, bisa yadda take fitar da kusan kaso 80% na motocin da ta samar zuwa ketare. Kasashen yamma suna zancen ‘yancin ciniki a lokacin da kayayyakinsu ke da fifiko, amma sun zargi kasar Sin da haifar da barazana ga kasuwannin duniya sabo da yadda kayayyakin da ta samar ke samun karbuwa. 

Lallai, bunkasuwar kasar Sin ce take haifar wa wasu kasashen yamma rashin jin dadi. Saurin bunkasuwar masana’antun samar da sabbin makamashi na kasar Sin na sa su damuwa, don haka ma suke shafa wa kasar Sin bakin fenti don neman dakile bunkasuwarta, tare da kiyaye babakeren da suka kafa a tsarin masana’antun samar da kayayyaki na duniya. Kasashen yamma sun yi ta fakewa da furucin nan na wai “kasar Sin na haifar da barazana”, don samar da dalili na yin kariyar ciniki.

Kasar Sin tana da ‘yancin tabbatar da bunkasuwarta, al’ummar Sinawa ma suna da ‘yancin tabbatar da rayuwa mai walwala. A yayin da suke kokarin cimma wannan buri, kasar Sin ta bunkasa da kara karfinta, amma ba don neman zarce wasu, ko haifar da barazana ga wasu, ko kuma maye gurbin wasu ba. A maimakon haka, tana son raba nasarorin da ta cimma tare da kasashen duniya, sabo da a ganinta, jirgi daya ne kasashen duniya suke ciki, kuma dole ne su hada kawunansu don tabbatar da kyakkyawar makoma ta bai daya.

Duk wanda ke neman shatile wasu, hakan ba zai kara masa saurin tafiya ba. (Lubabatu Lei)