logo

HAUSA

Bangaren kera motoci masu amfani da lantarki na kasar Sin ya yi kira ga EU da ya gudanar da bincike bisa adalci

2024-04-14 17:25:06 CMG Hausa

Kungiyar cinikayyar shige da ficen hajojin injuna da laturoni ta kasar Sin, ko CCCME a takaice, ta kira taron manema labarai a shekaran jiya ranar Jumma’a a Brussels, babban birnin kasar Belgium, inda ta yi kira ga kwamitin kungiyar tarayyar Turai wato EU, da ya kiyaye zaman daidaito da nuna adalci, kana ya aiwatar da komai ba tare da wata rufa-rufa ba, yayin da yake gudanar da bincike kan motoci masu amfani da makamashin wutar lantarki kirar kasar Sin. Kaza lika kungiyar ta CCCME ta jaddada cewa, duk wani matakin tallafawa cinikayya da EU za ta dauka, ba abun da zai haifar sai illata moriyar bangarori daban-daban.

Mataimakin shugaban CCCME Shi Yonghong, ya ce kamfanonin kera ababen hawa masu amfani da makamashin wutar lantarki na kasar Sin, sun samu nasara a kasuwannin duniya, bisa kwarewar da suke da ita, ba wai saboda dogara kan tallafin gwamnati da kwamitin EU ya fada ba. Ya ce ba’a nuna wa bangaren kasar Sin adalci ba, don haka binciken ya sabawa ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO.

Jami’in ya kara da cewa, ci gaban EU, gami da sana’ar kera ababen hawa masu amfani da makamashin wutar lantarki ta kasar Sin na dogara ne kan hadin-gwiwa ba rikici ba, don haka ya yi fatan kwamitin EU zai kirkiro kyakkyawan yanayi na matakan shawo kan sauyin yanayi, da yin sauye-sauye a fannin kiyaye muhalli, bisa la’akari da tabbatar da bunkasuwar sana’o’i da samar da hajoji yadda ya kamata a duniya. (Murtala Zhang)