logo

HAUSA

Kamfanin mai na NNPC ya jaddada goyon bayan sa ga kudirin shugaban Najeriya wajen samar da wadataccen gas a kasuwannin cikin gida dana kasashen ketare

2024-04-13 14:46:42 CMG Hausa

Babban shugaban kamfanin samar da albarkatun mai na tarayyar Najeriya Mele Kyari ya tabbatar da cewa sauye-sauyen da gwamanti ta samar a bangaren hada-hadar kudade ya haifar da tasiri mai ma`ana a harkokin cigaban kasar.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Legos, bayan da ya ziyarci shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu domin gasuwar salla, ya ce hakika aiwatar da tsare-tsaren tattalin arziki da shugaban ya bayar da umarni ya fara farfado da rushin kudaden kasar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Mr. Mele Kyari ya ce babu shakka manufofin gwamnati da suke kunshe a cikin kasafin kudi sun kawo canji mai ma`ana a kasuwar musayar kudade a Najeriya, ha ila yau irin hangen nesan shugaban kasa a fannin mai da iskar gas ya taka rawa sosai wajen kawo sauyin tattalin arzikin Najeriya da cigaban ta.

Shugaban kamfanin man na NNPC yace yana da kwarin gwiwar cewa salon tafiyar da sha`anin tattalin arzkin kasa da shugaba Tinubu ke bi, tare kuma da samun daidaito da cigaba a bangaren aikace aikacen kamfanin, gami kuma da samun kyakkyawan farashi a kan man da ake fitarwa zuwa kasuwannin duniya, ya sanya yanzu an kara samun wadatuwar albarkatun mai a cikin gida.

Ya ce sanin kowa ne man fetur shi ne abun da Najeriya ke tunkaho da shi wajen samun kudaden waje bayan ta sayar da shi a kasuwannin duniya.

“A yau an samu babban cigaba a kasuwar mai ta fuskar farashi, sannan kuma mun samu damar kaiwa ga wani matsayi a bangaren irin ayyukan da kamfanin na NNPC ke gudanarwa wanda hakan ke sanyawa muke samun Karin wadatuwar mai a kasar mu.”

Daga karshe ya sake bukatar `yan Najeriya da su rinka yi wa kamfanin kyakkyawan fata, kasancewar babban burin sa shi ne a samu wadatar albarkatun mai da iskar gas a kasar.(Garba Abdullahi Bagwai)