logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a kara kaimi a fannin diflomasiyya don kawo karshen rikicin Ukraine

2024-04-13 15:28:31 CMG Hausa

Wakilin kasar Sin ya yi kira da a kara kaimi a fannin diflomasiyya don kawo karshen rikicin Ukraine ta hanyar yin sulhu a siyasance a jiya Juma’a.

Rikicin na Ukraine ya ki ci ya ki cinyewa, wanda ya haddasa asarar rayuka da dama. Ci gaba da samar da makamai zuwa fagen daga, zai kara dagula hadarin da ke tattare da tabarbarewar rikicin, kuma ba zai taimaka daidaita lamarin da kawo karshen rikicin ba, a cewar Geng Shuang, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD. (Yahaya)