logo

HAUSA

Shugaban bankin duniya: Matakan kasar Sin na tinkarar sauyin yanayi abin burgewa ne

2024-04-13 16:19:54 CMG Hausa

A jiya Juma'a, shugaban bankin duniya Ajay Banga ya kira wani taron manema labaru, a gabanin taron lokacin bazara na bankin duniya, da hukumar ba da lamuni ta duniya IMF, na shekarar 2024. Inda Mista Banga ya ce, matakan da kasar Sin ta dauka a fannin tinkarar sauyin yanayin duniya, abin burgewa ne.

A cewar Ajay Banga, sauyin yanayi wani babban kalubale ne da daukacin bil Adama ke fuskanta. Ganin haka ya sa bankin duniya sanya buri na daga kason kudin da ya ware ma bangaren aikin tinkarar yanayi, don ya kai 45% kafin shekarar 2025. Mista Banga ya ce, ya tattauna batun rawar da kasar Sin ke takawa a fannin tinkarar sauyin yanayi, tare da shugabanni da manyan jami'ai na kasar Sin, a lokacin da ya kai ziyara kasar Sin a watan da ya gabata, inda matakan da kasar Sin ta dauka sun burge shi sosai.

Ya ce, kasar Sin ba ma kawai tana kokarin takaita gurbatar yanayi a fannonin aikin gona, da zirga-zirgar motoci, da ma masana'antu ba, hatta ma tana sa ido da bin bahasin yadda ake gurbata muhalli a ko da yaushe. Ban da haka kasar ta kan tura tawagogi na musamman zuwa wurin da ke fuskantar gurbacewa a kan lokaci, don daidaita matsalar da ke da bukatar a daidaita ta cikin gaggawa. (Bello Wang)