logo

HAUSA

Sin na goyon bayan yunkurin IAEA na tabbatar da tsaron tashar nukiliya ta Zaporizhzhia

2024-04-12 10:53:25 CMG Hausa

Kasar Sin ta bayyana goyon bayan ta ga yunkurin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, na tabbatar da kariya da tsaron tashar nukiliya ta Zaporizhzhia dake kasar Ukraine ko ZNPP, biyowa bayan hare haren jirgi maras matuki kan tashar a ranaikun Lahadi da Talata.

Da yake tsokaci kan hakan a jiya Alhamis, yayin taron musamman na majalissar jagororin kasashe mambobin hukumar su 35, wakilin dindindin na kasar Sin a hukumar ta IAEA Li Song, ya hakaito wani bangare na wata takardar sanarwa da Sin ta fitar a watan Fabarairun da ya gabata, dangane da matsayin kasar na warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa.

Li Song, ya ce Sin na adawa da amfani da karfin soji kan cibiyoyin nukiliya, ko wasu kayayyakin aiki masu nasaba da tashoshin, ya kuma jaddada bukatar kaucewa haifar da hadarin nukiliya.

Ya ce ko shakka babu, tabbatar da tsaron nukiliya a Ukraine ya ta’allaka ne da makomar warware rikicin kasar ta hanyar siyasa, don haka mista Li ya yi kira ga sassan kasa da kasa, da su ci gaba da yayata bukatar tattaunawar zaman lafiya, da karfafa gwiwa, da tallafawa dukkanin matakai masu dacewa na warware rikicin ta lumana, kana da kawar da kalubalen tsaron nukiliya da ake fuskanta.

Kasashen Rasha da Ukraine ne suka bukaci kiran taron na musamman, da nufin tattauna harin na tashar Zaporizhzhia na ranaikun Lahadi da Talata. Hara haren dai su ne na baya bayan nan, tun bayan wanda aka kai kai- tsaye kan tashar a watan Nuwamban shekarar 2022. Hukumar IAEA ta ce  ZNPP ita ce tashar nukiliya mafi girma a dukkanin fadin nahiyar Turai.

Bayan hare haren na baya bayan nan a jiya Alhamis, shugaban hukumar IAEA ya yi kira da a yi matukar kai zuciya nesa, duba da cewa hare hare kan ZNPP na matukar fadada hadarin nukiliya. (Saminu Alhassan)