logo

HAUSA

Sin: Hanyar siyasa ita ce kadai hanyar warware matsalar Ukraine

2024-04-12 11:42:10 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Geng Shuang, ya yi jawabi jiya Alhamis, yayin taron tattaunawa kan batun Ukraine na kwamitin sulhun MDD, inda ya jaddada cewa, hanyar siyasa ita ce kadai hanyar da ta dace a bi wajen warware matsalar kasar Ukraine.

Geng Shuang, ya ce kasar Sin ta damu matuka, da ganin yadda aka rikita, da tsawaita rikicin kasar Ukraine. Kaza lika ci gaban yaki a kasar, zai haddasa karin wahalhalu ga fararen hula, tare da yin barazana, haifar da kalubaloli ga yankin da ma kasashen duniya baki daya.

Geng Shuang ya kuma kara da cewa, kasar Sin ta sake yin kira ga bangarorin da abin ya shafa da su yi shawarwari kai tsaye, domin kaiwa ga matakin farko na warware matsalar ta hanyar siyasa, tare da sassauta yanayin tashe-tashen hankula a kasar, ta yadda za a tsagaita bude wuta cikin sauri.

Bugu da kari, ya kamata gamayyar kasa da kasa su dukufa kan aikin shiga tsakani, domin samar da damammaki masu kyau ga bangarorin da abin ya shafa, wajen yin shawarwari yadda ya kamata. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)