logo

HAUSA

Shugaban tarayyar Najeriya ya gana da hamshakin dan kasuwa Aliko Dangote domin lalubo hanyoyin rage hauhawar farashin kayayyaki a kasar

2024-04-12 19:28:29 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin hamshakin dan kasuwa Alhaji AliKo Dangote mamallakin katafaren matatar mai dake Legos ,inda suka tattauna a kan hanyoyin da za a samu raguwar hauhawar farashin kayayyakin masarufi a kasar.

Shugaban ya yi wannan ganawa ce a gidan sa dake birnin legos bayan da dan kasuwar ya kai masa ziyarar barka da sallah, yace duk wani kokari na gwamnati ba zai kai ga samun nasara ba idan dai babu hadin kan masu manyan masana`antu irin su Dangote.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cigaba dacewa, a yanzu haka tsare -tsaren tada komadar tattalin arzikin Najeriya ya kai wani mizani na cigaba sakamakon tasirin sauye- sauyen da aka bullo dasu a wannan bangare.

Yace babu shakka `yan Najeriya sun fuskanci kalubale mai tsanani a `yan watannin baya, tun lokacin da farashin kayayyaki suka yi ta yi tashin goron-zabi lamarin da yake da nasaba da rashin daidaiton farashi a kasuwannin canjin kudaden musaya, amma yanzu gwamanti ta samu nasara da kusan kaso 60.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar dacewa nan da ’yan wasu watanni masu zuwa komai zai zama tarihi a kasar, mutane zasu samu kansu a sabuwar rayuwa mai wadata.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan sun kammala ganawar da shugaban kasa, hamshakin dan kasuwa Alhaji ALiko Dangote ya yabawa gwamnatin tarayya saboda yadda tayi namijin kokari wajen farfado da darajar naira a kan dala, yace hatta a kasuwanni farashin kayayyaki ya tashi mutuka,saboda tsadar man gas da masu motocin dakon kaya ke fuskanta.

 Yanzu abun da muka zartar a matatar mu ta mai shine mun fara sayar da mai gas wato Diseil akan farashin naira dubu daya da dari biyu sabanin dubu daya da dari shida da hamsin.

“ Hakika wannan mataki da muka dauka ya yi tasiri sosai domin kuwa idan ka duba abun da a baya kake saye akan naira dubu 1,650 zuwa dubu 1,700 akan kowanne lita daya wannan hakika zai taimaka wajen rage hauhawar farashin kayayyaki cikin hanzari, kuma ina da tabbacin cewa da zarar an kawar da matsalar hauhawar farashin kayayyaki babu shakka nan da `yan watanni al`amura za su sauya”.(Garba Abdullahi Bagwai)