logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a kara hadin gwiwa a fannin cinikin kayayyakin fasahar sadarwa

2024-04-12 11:57:27 CMG Hausa

A jiya Alhamis, Sin ta gabatarwa kungiyar cinikayya ta duniya WTO shawarar ba da tabbaci ga aiwatar da yarjejeniyar fasahar sadarwa yadda ya kamata da karfafa karfinta a wasu bangarori masu nasaba, inda ta yi kira ga mambobin WTO da su kara hadin gwiwa a fannin cinikin kayayyaki masu alaka da fasahar sadarwa, bukatar da ta samu amincewa daga mambobin kungiyar ta WTO.

Sin ta nuna cewa, yarjejeniyar za ta samar da wani yanayi na cinikin duniya mai bude kofa, matakin da zai kara azamar cinikayyar kayayyaki masu kunshe da fasahar sadarwa, da ma yaduwar fasahohi a wannan bangare.

A cikin ‘yan shekarun baya, sana’o’i a wannan bangare sun samu saurin bunkasuwa, inda bangarori daban-daban ke fatan mambobin WTO za su kara hadin kai, don ayyukan kungiyar ma su tafi tare da zamani, da ma bayyana sabon halin da ake ciki a wannan fanni, kana da kara azamar yin cinikayya mai nasaba da hakan a wannan fanni.

Bisa hakan, kasar Sin ta baiwa WTO shawarar gabatar da rahoton shekara shekara game da cinikin kayayyaki masu alaka da fasahar sadarwa na duniya, da ma kokarin kawar da shingayen ciniki, da kara yaukaka mu’ammalar masu sana’o’in, da masu shirya tsare-tsare.  (Amina Xu)