logo

HAUSA

WTO ta yi hasashen farfadowar cinikayyar duniya sannu a hankali a bana

2024-04-11 13:45:38 CMG Hausa

 

Kungiyar cinikayya ta duniya WTO, ta fitar da sabon rahoton hasashe da kididdigar cinikayyar duniya. Rahoton ya yi hasashen cewa, a bana yawan kayayyakin da za a yi cinikayyar su za su karu da kashi 2.6%, adadin da zai kai kashi 3.3% a shekarar 2025.

To sai dai kuma WTOn ta yi gargadin cewa, rikice-rikice a wasu yankuna, da rashin kwanciyar hankali a wasu wurare, da rashin tabbacin manufofin tattalin arziki a wasu kasashe, za su haifar da cikas ga farfadowar tattalin arzikin duniya.

Babbar daraktar hukumar ta WTO Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa, ana kara azama wajen farfado da tattalin arziki, karkashin tsarin samar da kayayyaki mai kyau, da tsarin gudanar da ciniki tsakanin bangarori daban-daban mai karko. Lamarin da ya taimaka wajen kyautata zaman rayuwar jama’a matuka. Ta ce dole ne a kwantar da rikice-rikice a wasu wurare, da kawar da kalubalen gudanar da ciniki tsakanin wasu rukunoni kebantattu, ta yadda za a tabbatar da samun ci gaban tattalin arziki da karko.  (Amina Xu)