logo

HAUSA

An bude taron WTM Africa 2024 a birnin Cape Town

2024-04-11 11:22:46 CMG Hausa

An bude taron kasa da kasa na hada hadar kasuwanci a fannin tafiye tafiye na nahiyar Afirka ko “WTM Africa 2024”, a birnin Cape Town na Afirka ta kudu.

Taron wanda aka bude a jiya Laraba, ya hallara mashahuran jami’ai daga sassan duniya daban daban, wadanda ke taka rawar gani a fannin hada hadar tafiye tafiye, da yawon bude ido, ciki har da kwararru, da masu nune nune, da masu sayayya, da ‘yan jarida, inda ake tattaunawa, da nazarin damammakin dake akwai a sashen yawon bude.

“WTM Africa 2024”, wanda a bana ke gudana a karo na 10, muhimmin dandali ne na tattauna batutuwan da suka shafi tafiye tafiye, da yawon shakatawa a nahiyar Afirka, wanda kuma ke gudana tun daga jiya Laraba zuwa gobe Juma’a, a babban dakin taron jama’a na birnin Cape Town. Taron ya samar da dama ta bayyana fifikon sashen yawon bude ido na nahiyar, ta hanyar nune nune, da tarukan karawa juna sani, da bukukuwan mika lambobin karramawa.

Kaza lika a yayin taron na yini 3, wanda ya hallara wakilai sama da 7,000 daga sama da kasashen duniya 100, za a gudanar da tsararrun taruka sama da 9,500, da cudanya tsakanin sassa daban daban, da kuma kulla wasu harkoki na cinikayya.

Taron na “WTM Africa 2024”, na gudana ne karkashin babban taron makon tafiye tafiye na Afirka ko “Africa Travel Week 2024”, wanda ke gudana tsakanin ranaikun 7 zuwa 12 ga watan nan a dai birnin na Cape Town. Bugu da kari, mashirya taron “Africa Travel Week 2024”, sun ce makasudin sa shi ne yayata fahimta game da sashen yawon bude ido, da kulla karin huldodi, da bunkasa ci gaban kasuwanci a fannin. Har ila yau, taron na baiwa kamfanonin jiragen sama, da na jiragen ruwa, da otal otal, da mashirya tafiye tafiye, damar nuna hajoji masu inganci ga masu bukata na sassan kasa da kasa.

A cewar shafin yanar gizo na birnin Cape Town, tun fara gudanar da “WTM Africa 2024” a shekarar 2014, taron ya karbi bakuncin masu nune nune sama da 18,000, ya kuma samar da ayyukan yi sama da 17,000.    (Saminu Alhassan)