logo

HAUSA

Harin sama na dakarun Isra’ila ya hallaka iyalan babban jami’in Hamas

2024-04-11 16:55:40 CMG Hausa

 

Ofishin yada labarai na kungiyar Hamas, ya fitar da wata sanarwa a jiya Laraba cewa, sojin Isra’ila sun kai hari ta sama a wannan rana, kan wata mafakar ‘yan gudun hijira dake birnin Gaza, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 5, wadanda su ne iyalin babban jami’in Hamas Ismail Haniyeh.

Sanarwar ta kuma ce, wadannan mutane 5 sun hada da ‘ya’yan Haniyeh 3 da jikokinsa 2.

Game da hakan, Ismail Haniyeh ya shaidawa manema labarai na gidan talibijin din AL Jazeera na kasar Qatar cewa, Hamas ba za ta yi rangwame a cikin shawarwarin tsagaita bude wuta da za a yi tsakanin bangarorin biyu ba duk da mutuwar dangin nasa. (Amina Xu)