logo

HAUSA

Gwamnan Kano a arewacin Najeriya ya sha alwashin ci gaba da yaki da miyagun matasa masu tayar da zaune tsaye a cikin unguwanni

2024-04-11 11:14:58 CMG Hausa

 

Gwamnan jihar Kano dake arewacin Najeriya injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatin sa ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga yanayin zaman lafiyar da ake ciki a jihar ba.

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a jawabin da ya yi wa al`ummar jihar bayan kammala sallar idi, ya ce a `yan shekarun baya kafin kasancewarsa gwamna an yi ta samun barazanar tsaro a wasu unguwannin dake cikin birnin Kano, amma yanzu an dauki matakai masu karfi.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Injiniya Abba kabir Yusuf ya ci gaba da cewa daga cikin matakan da gwamantinsa ta dauka domin yaki da matsalar rigingimun daba a jihar sun hada da kyautata kafofin samun ilimi da kuma damarmakin ayyukan dogaro da kai ga matasan jihar.

Ya ce matsalolin rashin aikin yi da na ilimi na daya daga cikin manyan dalilan da suke sanya matasa shiga harkokin shan kwaya wanda daga nan ne kuma tunaninsu ke sauyawa zuwa ayyukan ta`addanci.

Gwamnan na jihar ta Kano bayan ya mika sakonsa na barka da salla ga al`ummar jihar da ma daukacin musulim Najeriya, ya ce watan azumin wata babbar makaranta ce dake haskawa al`umma rayuwa ta gari domin samun makoma mai kyau a nan duniya da kuma lahira.

“Ina rokon al`umma da su yi amfani da irin darussan da suka dauka wajen wannan ibada mai albarka, lallai ya zama wajibi akan mu mu cigaba da bautawa Allah da yin addu’o’i na zaman lafiya a jihar mu da wannan kasa tamu”

Shi ma a jawabin sa bayan kammalar salalr idin, mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero kira ya yi ga gwamnatoci a dukkan matakai da su himmatu wajen kai daukin rayuwa ga al`umma musamman a wannan lokaci da yanayin rayuwa ke kara tsada.

“Muna yiwa gwamnanmu da dukkan jami`an gwamnati da jama`a baki daya barka da sallah, muna kara jaddada kira ga gwamnatin Kano da gwamnatin tarayya da a cigaba da daukar matakai da za su dawo da aminci ga al`ummar mu da garuruwan mu”.(Garba Abdullahi Bagwai)