logo

HAUSA

MDD: Isra’ila na kakaba shingaye ga kayayyakin tallafi da ake fatan shigarwa Gaza

2024-04-10 11:14:31 CMG Hausa

 

Mai magana da yawun ofishin daidaita harkokin jin kai na MDD Jens Laerke, ya ce, kasar Isra’ila tana kawo cikas ga shigar da kayayyakin jin kai wadanda majalisar ta samar ga al’ummun yankin Gaza.

A cewarsa, a watan Maris da ya gabata, Isra’ila ta ki yarda da rabin rokon da aka yi mata, na shigar da kayayyakin jin kai zuwa arewacin zirin, lamarin da ya sa kayayyakin suka gaza biyan bukatun fararen hular yankin.

A nata bangare kuwa, Isra’ila ta yi ikirarin cewa, ba ta hana shigar da kayayyakin jin kai zirin na Gaza ba. (Amina Xu)