Shigar da Japan cikin kungiyar AUKUS kara kuskure manufar kungiyar ce
2024-04-10 21:27:06 CMG Hausa
“Wannan babbar barazana ce ga tsaron yankin.” A cikin ‘yan kwanakin nan, Amurka, Burtaniya, da Australiya sun sanar da shigar da Japan a cikin “AUKUS”, wanda ya tada hankalin al’ummar duniya. Wannan dai shi ne karo na farko tun bayan kafa kungiyar a watan Satumban shekarar 2021 da kasashen uku suka bayyana kawancensu da juna. Japan ta bayyana a hukumance cewa, ta amince da muhimmancin “AUKUS”. Amma yawancin jama’ar Japan suna sukar cewa, “AUKUS” tana watsi da damuwar dukkan bangarori kuma tana tallata mamaya, wanda zai kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Asiya da tekun Pasifik.
A takaice "AUKUS" na nufin “abokan hadin gwiwar tsaro na Amurka da Burtaniya da Australia”. A hakikanin gaskiya, wannan kawancen soja mai cike da tunani na yakin cacar baka bai dace da bukatun tsaron yankin ba, kuma bai zama dole a kafa shi ba tun farko. (Yahaya)