logo

HAUSA

Wasu ‘yan Najeriya sun gabatar da sakonninsu na barka da sallah ga ‘yan uwa da abokan arzikinsu

2024-04-10 11:07:23 CMG Hausa

Kasancewar yau take daya ga watan bikin karamar sallah, shugabanin da sauran al’ummar musulmi na cigaba da ziyartar juna tare da gabatar da sakonnin su na barka da sallah.

A lokacin da suke zantawa da wakilin sashen Hausa na CMG a tarayyar Najeriya Garba Abdullahi Bagwai, wasu daga cikin al’umomin sun bayyana farin ciki da nishadi bisa yadda Allah ya ba su koshin lafiyar ganin wannan rana ta bikin karamar sallah.

“Ni suna na Alhaji Abdulraheem Al-Aslim, dan kasar Sudan. Ina harkar kasuwanci a kasuwar Singa da Dawanau dake jihar Kano a Najeriya, ina mai mika gaisuwa na na barka da sallah ga duk ‘yan uwa na da abokan arziki dake Shumal da Khurdufan da Kazala, ina gaida dan uwana Abdulrazak da iyalansa da suke Alfashim da Niyala, da fatan an yi sallah lafiya, Allah ya maimaita mana, ina gaida sashen hausa na gidan rediyon kasar Sin.”

“Ni Alhaji Jedda, dan kasar Chadi, wanda nake harkar kasuwanci a tarayyar Najeriya, ina mika sako na barka da sallah zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki a Chadi, na farko dai ina gaida Ibrahim Saleh Ramat na unguwar Andukkum da aboki na Alhaji Tom na unguwar Radina da ‘yan uwa da suke Bittalbagra, da fatan duk kun yi sallah lafiya, Allah ya maimaita mana. Na gode. Ina mutukar godiya da gidan rediyon kasar Sin.”

“Assalamu alaikum, suna na Yusuf Sulaiman Ahmed daga Kano, ina mika sakon barka da salla ga ilahiri al’ummar musulmin duniya, kuma ina mana fatan mun yi sallah lafiya, kuma Allah ya karbi ibadun mu da muka gudanar a lokacin watan ramadana, ina gaida dan uwana yaya na Najib Sulaiman da kane na Bashir Sulaiman da kuma kanwa ta Rukayya Sulaiman da kuma aboki na Salmanu Adam, sai kuma aboki na da yake a birnin Abuja Abdulkadir Yusuf, ina kuma mika sakon gaisuwa ga ma’aikatan gidan rediyon kasar Sin wato CRI.(Garba Abdullahi Bagwai)