logo

HAUSA

An fara shirye-shiryen gudanar da babban zabe a Sudan ta Kudu

2024-04-10 11:16:23 CMG Hausa

 

Gwamnatin kasar Sudan ta kudu ta sanar da fara shirye-shiryen gudanar da zabukan ‘yan majalisun dokokin kasar a watan Disamban karshen shekarar nan, zaben da zai kasance na farko a kasar dake gabashin Afirka tun bayan samun ‘yancin kanta a shekarar 2011.

Bayan kawo karshen yakin basasar kasar a shekarar 2018, da samun ‘yancin kai a 2011, Sudan ta Kudu ta tsara gudanar da zabukan kafin watan Fabrairun shekarar 2023 da ta gabata. To sai dai kuma daga bisani, gwamnatin rikon kwaryar kasar da ‘yan adawa, sun amince da dage zaben zuwa karshen shekarar nan ta 2024.  (Saminu Alhassan)