logo

HAUSA

Masu zanga-zanga sun dakatar da taron sauraren bahasi game da kasafin ma'aikatar tsaron Amurka

2024-04-10 11:12:18 CMG Hausa

 

Majalisar dattawan kasar Amurka ta gudanar da taron sauraren bahasi game da kasafin ma'aikatar tsaron kasar na shekarar 2025, wanda adadinsa ya kai dalar Amurka biliyan 850. Yayin zaman na jiya Talata, masu zanga-zanga sun rika dakatar da taron.

Halin jin kai a zirin Gaza na kara kamari, sakamakon tsanantar rikicin dake wakana a wannan karo tsakanin Palasdinu da Isra’ila. Karin Amurkawa ciki har da wasu mambobin majalisun dokokin kasar sun aza ayar tambaya kan manufar tallafawa Isra’ila da makamai da gwamnatin Amurka ke dauka. Ban da wannan kuma, jam’iyyun Dimokirat da Republikan, suna matukar sabawa da juna game da batun samarwa Ukraine da Isra’ila makamai. (Amina Xu)