logo

HAUSA

Yau al’ummar musulmi a tarayyar Najeriya suke gudanar da bikin karamar sallah

2024-04-10 11:23:26 CMG Hausa

Yau al’ummar musulmi a tarayyar Najeriya suka bi sahun na sauran kasashen musulmin duniya wajen gudanar da bikin karamar sallah bayan karewar watan azumin Ramadan.

Tun dai a ranar talata 9 ga watan mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya tabbatar da yau Laraba a matsayin 1 ga watan Shauwal hijira ta 1445, wanda ya yi daidai da 10 ga watan Afrilun 2024.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Cikin wata sanarwa da shugaban kwamatin mashawarta a kan harkokin addinin Musulunci dake fadar sarkin musulmi Farfesa Sambo Wali Junaidu ya fitar tun a ranar ta Talata, ta nuna cewa cika azumi 30 ya biyo bayan rashin ganin watan Shauwal ne a ranar Litinin 8 ga wata.

A sakonsa na sallah ga daukacin al’ummar musulmin kasar, sarkin musulmin yayin fatan jama’a za su amfani da darussan da suka koya a cikin watan na Ramadan da muka yi ban kwana da shi.

Shi ma a sakonsa na murnar sallah ga ‘yan Najeriya, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce godiya ya yi ga Allah da ya nuna mana karshen watan na Ramadan cikin walwala da wadata, inda ya yaba mutuka bisa yadda al’umma suka himmatu a lokutan azumin wajen yiwa kasar addu’ar dorewar zaman lafiya da ingantuwar tattalin arziki.

Ya ce hakika gwamnati ta ga hasken irin addu’o’in da jama’a suka yi mata, saboda yadda tun daga farkon watan na azumi, al’amuran tattalin arzikin kasa suka fara daidaituwa sosai.

Ta bangaren tsaro kuwa, tun daga daren ranar Talata da ta gabata ne, hukumomin tsaron kasar suka dauki managartar matakan tabbatar da tsaro a kowanne sashe na kasar domin tabbatar da ganin an gudanar da shagulgulan sallah cikin natsuwa ba tare da fargabar wani abu ba . (Garba Abdullahi Bagwai)