logo

HAUSA

Ana fatan Amurka za ta sauke nauyin dake wuyanta bayan ziyarar Janet L. Yellen a Sin

2024-04-09 11:20:28 CMG Hausa

 

Sakatariyar baitilmalin kasar Amurka Janet L. Yellen za ta kammala ziyarar aikinta a nan kasar Sin a yau Talata. Yayin ziyarar, Sin da Amurka sun yi mu’ammala tsakanin manyan jami’ai da bangarori daban daban, inda suka amince da tabbatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, tare kuma da cimma daidaito wajen kara azama kan bunkasuwar tattalin arziki da yin hadin gwiwa a hada-hadar kudi. A cewar Janet L. Yellen, Amurka da Sin kamata ya yi su daidaita huldarsu ta bangaren tattalin arziki bisa nauyin dake rataye a wuyansu, tare kuma da bayyana matsayin kasar na yin watsi da ra’ayin katse hulda da Sin.

To, Janet L. Yellen ta ambaci kalmar nauyi, mene ne ainihin ma’anar sauke nauyi? Ba kawai Amurka ta sauke nauyin dake wuyanta wajen tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikinta da mai da hankali kan muradunta kawai ba, dole ne ta kara kawo wa kamfanoni da al’ummomin kasashen biyu alheri, har ma da yin tunani kan yadda za a samu moriyar juna, da tinkarar kalubalen duniya baki daya, da ciyar da tattalin arzikin duniya gaba. Ta yaya za a tabbatar da wadannan abubuwa? Akwai wasu ma’aunonin da za a kimanta abin da Amurka ke gudanarwa, na farko, dakatar da siyasantar da batun tattalin arziki, kuma kada ta tada zaune tsaye bisa hujjar kiyaye tsaro, da kuma yin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka bisa dokokin tattalin arziki da ka’idojin kasuwa.

An ruwaito cewa, Janet L. Yellen ta bayyana kin amince da ra’ayin katse hulda da Sin, yayin da take ziyara a birnin Guangzhou da Beijing. Sin na maraba da hakan sosai, tana mai fatan Amurka za ta dauki matakan a-zo-a-gani.

A bana, an cika shekaru 45 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu. Tarihi ya shaida cewa, muradun Sin da Amurka na da dogaro da juna. Zurfafa hadin kan tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen 2 ya dace da muradunsu, kuma ya amfana wa bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya. Ko Amurka za ta sauke nauyin dake wuyanta, bari mu jira. (Amina Xu)