Kasar Sin Ta Hau Kujerar Naki A Kwamitin Sulhun MDD Don Tabbatar Da Adalci A Duniya
2024-04-09 10:37:17 CMG Hausa
Mukaddashin babban jami’in zaunanniyar tawagar kasar Sin a MDD a jiya Litinin ya yi karin haske kan matakin da kasar Sin ta dauka na hawan kujerar naki a kwamitin sulhu na MDD, musamman dangane da daftarin kudurin da aka gabatar a ranar 22 ga watan Maris, inda ya jaddada wajibcin tabbatar da adalci a duniya.
Da yake jawabi a babban taron MDD da ke muhawara kan hawan kujerar naki a kwamitin sulhun, Dai Bing, mukaddashin babban jami’in zaunanniyar tawagar kasar Sin a MDD ya bayyana dalilin da ya sa kasashen Sin da Aljeriya da Rasha suka yi kakkausar adawa a ranar 22 ga watan Maris kan daftarin kudurin da Amurka ta gabatar kan Gaza.
Dai dai ya isar da buri na gama-gari na kiran samar da zaman lafiya da al’ummar kasa da kasa ke yi tun bayan barkewar rikicin Gaza.
Ya yi kakkausar suka ga Amurka kan cikas da take kawowa ga tsagaita bude wuta da kuma daftarin kudurin da ta gabatar, wanda a cewarsa, ya kaucewa batun tsagaita bude wuta, da yunkurin gindaya sharudda na tsagaita bude wuta, da kuma neman yin amfani da kwamitin sulhun wajen amincewa da munanan manufofin Washington.
Dai ya bayyana kuri’ar kin amincewar da kasar Sin ta jefa, a matsayin wata manufa ta tabbatar da adalci, lamarin da ya tilasta wa Amurka amince da gazawarta ta kara dakile ci gaban da MDD ta samu wajen tabbatar da zaman lafiya.
Dai ya kuma bayyana amincewa da kudurin da ya biyo baya mai lamba 2728, wanda ya bukaci a tsagaita bude wuta nan take, a matsayin wata nasarar da aka cimma a dalilin tsayin dakar kasar Sin.
Da yake kammala jawabin nasa, Dai ya sake tabo ainihin batun rikicin Falasdinu da Isra'ila, wato batun samar da kasashe biyu da ba a cimma ba. Ya kuma jaddada goyon bayan kasar Sin ga kasancewar Falasdinu mamba a MDD, kana ya bukaci kwamitin sulhu da ya gaggauta daukar mataki kan wannan batu. (Yahaya)