logo

HAUSA

Kwamitin sulhun MDD ya sake bincike kan rokon Palasdinu na neman shiga majalisar

2024-04-09 13:48:29 CMG Hausa

Jiya Litinin, kwamitin sulhu na MDD ta sake bincike kan rokon da Palasdinu ta gabatar na neman zama mambar majalisar, kuma ya yanke shawarar mika wannan batu ga kwamitin dindindin mai karbar sabbin mambobi.

Bisa kundin tsarin mulkin MDD, shigo da sabuwar mamba na bukatar gabatarwa daga kwamitin sulhun, da amincewa daga babban taron MDD. Ban da wannan kuma, dole ne mambobin kwamitin a kalla 9 su amince da batun, kuma ba wata kasar da ke da kujerar dindindin ta MDD da ta ki amincewa da haka, kana ana bukatar kuri’un amincewa daga fiye da kashi 2 bisa kashi 3 na dukkan mambobin MDD a babban taron majalisar.

Palasdinu ta mikawa babban sakataren MDD a waccan lokaci Ban Ki-moon, rokon shiga majalisar a watan Satumba na shekarar 2011, ba tare da samun amincewa ba. A ran 29 ga watan Nuwamba na shekarar 2012, babban taron majalisar ta zartas da kudurin baiwa kasar matsayin mai sa ido a majalisar. (Amina Xu)