logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da shirin rabon kayan abinci kyauta ga `yan kasar

2024-04-09 14:01:31 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da shirin rabon kayan abinci kyauta ga `yan kasa a jihar Sokoto dake arewacin kasar.

A lokacin da yake kaddamar da shirin rabon kayan abincin ministan bunkasar harkokin noma na tarayyar Najeriya Sanata Abubakar Kyari ya ce adadin buhuna dubu 26 da 404 ne aka fara rabawa ga masu karamin karfi a jihar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Kayayyakin abincin sun kunshi buhunan Masara, da Gero da kuma Dawa.

Sanata Abubakar kyari ya yi alkawarin cewa gwamnatin  tarayyar za ta fito da dukkannin kayayyakin abincin dake ajiye a rumbunanta domin cike gibin karancin abincin da talakawan kasar ke  fuskanta.

Ministan ya ce ba jahar Sokoto ce kadai ta amfana da kayan abincin ba, shirin ya karade kowanne sashe na Najeriya ciki har da birnin Abuja, lamarin da ya bayyana da cewa zai taimaka mutuka wajen saukaka wa al`umma kalubalen koma bayan tattalin arziki.

“Ina farin cikin ganin yadda farashin kayayyakin abinci ke kara saukowa tare kuma da wadatar sa a kasuwannin kasar, kuma wannan ya faru ne sakamakon shigowar da gwamnati take yi akai-akai cikin `yan makonnin nan wajen kai daukin abinci a dukkan sassan kasar”

Ya ce adadin tan dubu 42 na kayan abinci shugaban kasa ya amince a fito da su daga ma`ajiyar abinci na kasar.

A jawabin sa gwamnan jihar Sokoto Alhaji Ahmed Aliyu ya tabbatar da cewa babu shakka al`umma suna cikin halin matsin rayuwa sakamakon matsalolin tattalin arziki.

“A madadin al`umma da gwamnatin jihar Sokoto ina mika sakon godiyata ga shugaban kasa saboda yadda yake bayar da tallafi ga al`ummar jihar a duk lokacin da aka mika bukata”

Gwamnan ya tabbatar da bin ka`idoji da sharudodin da aka gindaya wajen rabon kayan a jihar.(Garba Abdullahi Bagwai)