Jakadan Sin a Nijar ya gana da shugaban kasar
2024-04-09 19:57:03 CMG Hausa
Jakadan kasar Sin a janhuriyar Nijar Jiang Feng, ya gana da shugaban kasar Abdourahamane Tchiani, a jiya Litinin, inda suka yi tattaunawa mai ma’ana game da bunkasa dangantakar Sin da Nijar, tare da karfafa hadin gwiwa a fannin albarkatun mai.
Yayin zantawar ta su, jakada Jiang Feng ya ce hadin gwiwar Sin da Nijar a fannin raya yankunan hakar mai, ya haifar da kyakkyawan sakamako cikin shekaru 20 da suka gabata. Kaza lika a halin da ake ciki yanzu, zango na 2 na aikin fitar da danyen mai daga mahakar Agadem ya shiga muhimmin mataki. Ya ce Sin na aiki tare da Nijar, wajen ingiza aiwatar da aikin yadda ya kamata, tare da ci gaba da fadada sassan hadin gwiwa tsakanin kasashen 2, da cimma moriyar juna, da bunkasa hadin gwiwar cin gajiya tare tsakanin su.
A nasa bangare kuwa, shugaba Abdourahame Tchiani, cewa ya yi yayin da ake gina yankin na hakar mai, Sin ta magance manyan matsaloli, da horas da tarin ma’aikata ‘yan Nijar. Ya ce kyakkyawan sakamakon hadin gwiwar kasashen biyu ya tabbatar da cewa, hadin gwiwa da Sin yana tafiya bisa tafarin kare moriyar al’ummun Nijar. Don haka a cewar shugaban kasar, Nijar a shirye take ta samar da yanayi mai kyau na zuba jari a kasar ga kamfanonin kasar Sin. (Saminu Alhassan)