logo

HAUSA

Jakadun kasashen duniya sun yi buda baki da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a birnin Abuja

2024-04-08 11:26:54 CMG Hausa

 

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kara isar da bukatar samun zaman lafiya a sassan da suke fama da yake-yake musamman a Afrika da sauran nahiyoyin duniya baki daya.

Mr. Bola Ahmed Tinubu ya bukaci hakan ne a fadarsa dake birnin Abuja yayin buda baki da jakadun kasashen duniya da shugabannin kungiyoyin kasa da kasa, ya ce akwai bukatar shugabannin kasashe su karkatar da hankulansu wajen tabbatar da zaman lafiyar duniya baki daya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaban na tarayyar Najeriya ya ce lokacin ya yi da ya kamata  shugabannin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa na duniya su hada kan su tare da fito da wasu sahihan matakai na diplomasiyya da za su samar da mafita ta karshe wadda za ta dakile tasirin kungiyoyin ‘yan ta’adda da na masu tada kayar baya kana da rikice-rikien kabilanci da na addini.

Shugaban ya jaddada mahimmancin hakuri da juriya a matsayin manyan sinadaran samar da dauwamamen zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’ummar duniya, wanda hakan na daga cikin darasin watan azumin Ramadan.

“Na ji dadin kasancewar ku a nan, inda muke musayar bayanai a tsakanin mu, amma ya kamata a cikin zuciyarmu mu saka tausayi da jin kan marasa galihu wadanda ba su da wadata domin da su ne za mu hadu mu samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, ba za a taba samun wadatuwar tattalin arziki ba ba tare da zaman lafiya ba.”

Daga karshe shugaban na tarayyar Najeriya ya bukaci jakadun kasashen da su isar da sakonsa na zaman lafiya ga shugabannin kasashensu.(Garba Abdullahi Bagwai)