logo

HAUSA

Kamfanonin EV na kasar Sin ba sa dogaro da tallafi

2024-04-08 17:04:11 CMG Hausa

Wang Wentao, ministan kasuwanci na kasar Sin ya bayyana a jiya Lahadi cewa, saurin bunkasuwar kamfanonin kera motocin lantarki (EV) na kasar Sin, sakamakon kirkire-kirkiren fasahohin zamani ne, da kyakkyawan tsarin samar da kayayyaki, da ingantacciyar takara a kasuwa, ba tallafi ba. Zargin da Amurka da Turai ke yi na samar da motocin fiye da kima ba shi da tushe, a cewarsa.

Zargin da Washington da Turai suka yi na barazanar "girman karfin masana'antun" na kasar Sin wajen samar da hajoji fiye da kima da kuma zargin rashin adalcin cinikayya da kamfanonin Amurka da Turai, ya samo asali ne daga maganganunsu masu tayar da hankali da kuma zurfin rashin fahimta game da kasuwar kasar Sin. Amurka na ganin cewa sassan tattalin arzikin kasar Sin na samun goyan baya da tallafi na wucin gadi, kuma yana rage damammakin ga bunkasuwar kasuwannin Amurka har ma da kawar da ayyukan yi. Yayin da a hakikanin gaskiya, kasar Sin ba ta taba tsunduma cikin harkokin cinikayyar da ba ta dace ba ko nuna son kai ga kamfanoni ba.  Kasar Sin ita ce jagora a fannin samar da motocin lantarki wato EV, na'urorin hasken rana, batura, saboda kwarewarta da dorewar sabbin kirkire-kirkirenta, da karuwar bukatun hajojinta daga ko'ina cikin duniya. Hajojin kasar Sin masu inganci suna da fifiko sosai a kasuwannin duniya kuma suna biyan bukatun abokan cinikayya a ketare.

Duk wanda ya lura da karfin tattalin arzikin kasar Sin, ko shakka babu zai fahimci cewa, kasar na bin tsarin 'yancin cinikayya, da ka'idojin WTO, da tsarin cinikayya na duniya.  Kasar Sin ba za ta taba yin amfani da dabarun kasuwancin da ba su dace a kan kamfanonin ketare ko kuma ta yi babakere ba. 

Ban da haka, bunkasuwar masana'antun EV na kasar Sin ta ba da muhimmiyar gudummawa wajen tinkarar sauyin yanayi a duniya, da samar da sauye-sauye don kiyaye muhalli da rage hayakin Carbon mai dumama yanayi. (Yahaya)