Isra’ila ta janye sojojinta daga kudancin zirin Gaza
2024-04-08 14:21:27 CMG Hausa
Kafofin yada labarai na kasar Isra’ila sun ba da labari a jiya Lahadi cewa, rundunar sojin kasar ta janye jiki daga yankin Khan Younis dake kudancin zirin Gaza, wata karamar rundunar soja kawai Isra’ila ta bari a yanki na Gaza ya zuwa yanzu. Ministan tsaron kasar Isra’ila Yoav Gallant ya shaida a wannan rana cewa, janyewar sojojin kasar ya kasance matakin share fage ne na sauran ayyuka, ciki har da aikin soja da za a gudanar a birnin Rafah dake kudancin Gaza.
Gidan talabijin na Alkahira na kasar Masar ya ba da labari a yau Litinin cewa, an samu ci gaba a shawarwarin da aka gudanar a wani sabon zagaye a birnin kan tsagaita bude wuta a zirin Gaza, inda bangarori masu ruwa da tsaki suka kai ga cimma matsaya daya. Labarin ya ruwaito bayani daga bangaren Masar na cewa, tawagar Isra’ila da ta Hamas sun isa birnin a jiya Lahadi don yin musanyar ra’ayi da bangarori daban-daban. Ya zuwa yanzu, tawagar Hamas ta bar Alkahira, amma ana sa ran za su koma a cikin kwanaki biyu, inda za su kai ga cimma matsaya daya kan ayoyin yarjejeniya na karshe.
Kamfanin dillancin labarai na Jordan ya ba da labari cewa, Jordan ta tura zuwa zirin Gaza motoci 105 na dakon tallafin abinci a ran 7 ga wata, wannan shi ne ayarin motoci mafi girma da Jordan ta tura tun barkewar rikici tsakanin Palasdinu da Isra’ila a wannan karo. (Amina Xu)