logo

HAUSA

Wannan Sabuwar Sana'a Ta Nuna Ra'ayi Daya Na Afrika Da Sin

2024-04-08 17:41:50 CMG Hausa

Yau na ga wani bayani mai taken “Shin sabbin tashoshin canza batura na kasashen Afirka za su ba kasar Amurka kunya?”, da aka nuna a kan shafin yanar gizo na Electrek na kasar Amurka, mai gabatar da bayanai masu alaka da motoci. Wanda ya yi bayani kan sabuwar sana’ar kera babur din wutar lantarki da samar da tashoshin canza batura, da ke tasowa a kasashen Afirka. Cikin bayanin, an ce, ingancin fasahar canza baturan babur na Afirka ya wuce na kasashen dake arewacin nahiyar Amurka, kana fasahar na kan hanyar tasowa cikin matukar sauri, a kasashe na Afirka.

Na karanta wannan bayani, kuma na yi mamakin yadda ci gaban wata sana'ar kasashen Afirka ya sa Amurkawa kaskantar da kansu, don haka na karanta karin wasu bayanai masu alaka da batun. Daga baya na gano cewa, da gaske ne tsarin yayata fasahar babur din wutar lantarki na kasashen Afirka yana da inganci, wanda kuma ya dace da yanayin da kasashen suke ciki.

Cikin shekarun nan, kasashen Kenya, da Benin, da sauran takwarorinsu dake nahiyar Afirka, suna kokarin samar da damammakin raya bangaren kera da amfani da babur din wutar lantarki, don neman kare muhalli, da tsimin kudin musaya da ake kashewa wajen shigar da man fetur daga ketare. Sa'an nan wasu kamfanoni na kasashen sun yi la’akari da yadda aka fi yin amfani da babur wajen samar da hidimar kwashe fasinjoji a kasashen Afirka, inda suka samar da nau'ikan babura da suke da karfin dakon kaya mai nauyi, da isasshiyar wutar lantarki da ta ba da damar zuwa wuri mai nisa. Ban da haka, sun kafa dimbin tashohin canza batura ga babura, a garuruwan kasashen Benin, da Togo, da Rwanda, da Kenya, da dai sauransu.

Bisa alkaluman da wasu kamfanonin kasar Kenya suka gabatar, an ce, mutumin da ya yi amfani da babur din wutar lantarki wajen kwashe fasinjoji ko kuma kai kaya, zai bukaci canza batir sau 2 duk rana, inda zai dauki tsawon lokaci kimanin minti 6, da kudi kimanin dalar Amurka 4. Ka ga zai fi araha idan an kwatanta da babur mai kona mai. Ta wannan hanya, masu tuka Okada da masu kai kaya sun samu karin kudin shiga, kamfanoni masu alaka ma sun bude wata sabuwar sana’a cikin nasara, yayin da gwamnati a nata bangare ta samu damar raya tattalin arziki, da rage iskar dumama yanayin da ake fitarwa, kowa ya samu biyan bukata.

Wannan al'amari ya burge ni a fannoni 2, har ma ya sa ni alfahari. Na farko shi ne, na ga yadda fasahohin kasar Sin suka samar da gudunmowa ga ci gaban sana'ar babur din wutar lantarki a kasashen Afirka.

Kun san kasar Sin ta dade tana zuba kudi don raya bangaren kimiyya da fasaha, ta yadda ta samu dimbin fasahohin zamani dake kan gaba a duniya, musamman ma a fannin fasahohin kare muhalli. Yanzu a fannin cinikin kasa da kasa, wasu nau'ikan kayayyakin da kasar Sin ke samarwa na samun karbuwa sosai a mabambantan kasashe, wadanda suka hada da motocin wutar lantarki, da batiri na Lithium, da na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana, da dai sauransu. Ganin haka ya sa kamfanonin kasashen Afirka dake neman samar da babur din wutar lantarki zuwa kasar Sin don neman samun abokan hulda. A halin yanzu, wasu kamfanonin Afirka dake kan gaba a wannan fanni, irinsu Spiro na kasar Benin, da Kofa na kasar Ghana, da dai sauransu, dukkansu sun kulla huldar hadin gwiwa tare da kamfanoni masu fasahohin sabbin makamashi na kasar Sin.

Sa'an nan abu na biyu da ya burge ni shi ne, yadda ake kokarin raya sana'ar babur din wutar lantarki a kasashen Afirka, ya nuna ra'ayi daya da kasashen Afirka da kasar Sin suke da shi, ta fuskar raya sabbin fasahohi.

Wata babbar manufar kasar Sin ita ce, “Raya sabon karfin samar da kayayyaki da hidimomi masu karko, bisa yanayin da ake ciki”, wadda ta kunshi fannoni guda 2: Na farko, shi ne a dinga rungumar sabbin fasahohi, don sa kaimi ga ci gaban tattalin arziki. Sa'an nan, na biyu shi ne, a kaddamar da sabuwar sana'a bisa yanayin da wani wuri yake ciki, da bukatu dake akwai a kasuwanninsa.

Idan mun yi bitar manufar kasashen Afirka, za mu ga suna da tunani kusan iri daya. Inda suke kokarin shigar da sabbin fasahohi, amma ba tare da kwaikwayon tsare-tsaren kasashen waje kai tsaye ba. Maimakon haka, sun gabatar da tsari na kansu ne bisa la’akari da bukatun kasuwannin gida, inda suka fara sauya babur din mai daukar fasinjoji da kayayyaki zuwa irin na wutar lantarki, da kafa tashohin canza batiri don daidaita matsalar rashin damar cajin batiri a kasashen Afirka.

Ma iya cewa yadda kasashen Afirka da kasar Sin suke da tunani iri daya a fannin raya sabbin fasahohi, ya nuna kokarin da kasashe masu tasowa suke yi, na neman hanyar raya tattalin arziki ta kansu, wadda ta dace da ainihin yanayin da suke ciki.

A karshen bayanin shafin yanar gizo na Electrek, an ce, “ Watakila wata rana, kasar Amurka za ta koyi wasu dabaru na kasashen Afirka, na samar da ababen hawa na wutar lantarki masu araha, da saukin sarrafawa, da tsari mai kima. Ko kuma za mu iya ci gaba da tuka manyan motocin SUV na wutar lantaki, da nauyinsu ya kai Lb 8000 ( kwatankwacin kilo 3629), mu je kasuwa, tare da fuskantar babban hadari na kashe wani mutum dake tafiya a dab da titin mota.”

Hakika ko kasar da ta saba da samar da tsare-tsare domin sauran kasashe su bi ma, ya kamata ta tantance tsarin kanta, da sake tunani kan mene ne tsare-tsare masu dacewa. (Bello Wang)