logo

HAUSA

Kasar Sin na kokarin kiyaye muhalli ta hanyar kafa yankunan kare sassan doron kasa masu kayatarwa ko “Geoparks”

2024-04-08 07:06:40 CMG Hausa

Yayin da duniya ke kara himmatuwa wajen kare muhalli, da kyautata muhallan zaman bil adama, da sauran halittu dake kewaye da shi, mahukunta a kasashe da yankuna da dama na ta kara azamar aiwatar da matakai daban daban na samar da karin yankunan kare sassan doron kasa masu kayatarwa ko “Geoparks”. 

“Geoparks” na nufin wani yanki mai kunshe da sassan doron kasa masu ban sha’awa. yankin zai iya zama na tsauni ko tsaunuka, ko wurin da ruwa yake kwance ko yake gudana, ko yankin da dutse ke aman wuta, da ma inda kasa ke zaizayewa, da jerin wasu duwatsu masu ban sha’awa, da dazuzzuka masu kayatarwa da sauran su.

Hukumar kula da ilimi, kimiyya da al'adu ta MDD (UNESCO) ce ke ayyana wurare daban daban a duniya a matsayin Geoparks, bayan tantance ingancin su, da kimar gadon su, domin yayata ilmantar da jama’a game da muhimmancin wuraren ta hanyar yawon bude ido.

Wadannan wurare suna iya zama masu muhimmanci ta fuskar daraja a idanun kasa da kasa, suna zama masu ban sha’awa ga maziyarta, suna suna ba da gudummawa ga binciken kimiyya ko fa’idar raya ilimi.

Akwai irin wadannan Geoparks masu matsayin kasa da kasa har 213 da UNESCO ta ayyana a kasashe 48. Kuma a baya bayan nan UNESCOn ta kara wurare 6 na cikin kasar Sin cikin jerin Geoparks da take lasaftawa a hukumance.

Sabbin Geoparks din na Sin su ne Tsaunin Changbaishan na lardin Jilin, da babban ginin ajiye kayan tarihi na Enshi Grand Canyon da babban kogon dutse na Tenglongdong, da Geoparks na Linxia, da na Longyan, da na Wugongshan da na Xingyi. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Faeza Mustapha)