logo

HAUSA

Jami’ar bankin Zanaco: Jarin da Sin ke zubawa a Zambia na bunkasa tattalin arzikin kasar

2024-04-07 15:16:11 CMG Hausa

Shugabar bankin Zanaco mai gudanar da hada hadar kasuwanci a kasar Zambia, Mukwandi Chibesakunda, ta ce hada hadar kasuwanci da jarin da sassan kasar Sin ke zubawa a Zambia, suna kara bunkasa tattalin arzikin kasar. Ta ce alkaluma sun nuna yadda wadannan harkoki ke taka muhimmiyar rawa, wajen daga matsayin ci gaban kasar, da samar da karin guraben ayyuka da ababen more rayuwa.

Uwar gida Chibesakunda, wadda ta bayyana hakan yayin wata liyafa da ta shiryawa Sinawa abokan huldar bankin na Zanaco a ranar Juma’a, ta ce hadin gwiwar kamfanonin kasar Sin da sassan hada hadar kasuwanci na Zambia, ya yaukaka tattalin arzikin kasar, tare da bunkasa hada hadar cinikayya tsakanin kasashen biyu.

Jami’ar ta kara da cewa, bankin su ya yi imani da muhimmancin hadin gwiwar sassan biyu, ya kuma sha alwashin goyon bayan bunkasa hada hadar kasuwancin Sinawa a Zambia.

Ta ce baya ga bunkasa fannonin tattalin arziki, jarin da sassan kasar Sin ke zubawa a Zambia, na kuma ba da damar karfafa kwarewar ayyuka da musayar fasahohi.   (Saminu Alhassan)