logo

HAUSA

Shugaban Tinubu na tarayyar Najeriya ya gana da jagororin manyan kamfanonin `yan kasuwar kasar dana kasashen waje

2024-04-07 14:50:27 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce tattalin arzikin kasar yana kan gabar sauyi mai ma`ana, a don haka ya bukaci hadin kan kamfanoni masu zaman kansu domin samun cigaba mai dorewa da wadata.

Ya bukaci hakan ne a birnin Abuja lokacin da ya jagoranci taron shan ruwa da shugabannin kamfanonin gwamnati dana `yan kasuwa dake kasar, inda ya kara jaddada jin dadin sa bisa irin hadin kan da `yan kasuwar kasar ke bayarwa wajen sake farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaban na tarayyar Najeriya haka kuma yayi alkawarin cewa gwamnatin sa zata himmatu sosai wajen hada kai da `yan kasuwar kasar da kuma baki `yan kasashen wajen da suka zuba jarin su a kasar a dukkan wasu shirye shirye raya tattalin arzikin kasa da gwamnati ta bullo da su.

Ya ce zai kara jajircewa sosai wajen don ganin ya cimma muradun sa, domin tabbatar da kyakkyawan zaton da al`ummar kasar suke masa.

Ya cigaba da cewa muddin dai aka samu rauni a harkokin kamfanonin masu zaman kansu, tabbas ba za a samu cigaba da wadata da kuma kofofin samun aikin yi ba a kowacce kasa, a don haka kamar yadda shugaban ya fada, yana mutukar alfahari da kwazo da kamfanonin masu zaman kansu ke nunawa a sha`anin cigaban tattalin arzikin Najeriya.

Yace babban abin da gwamnati ta sanya a gaba yanzu a kokarin tada komadar tattalin arziki shi ne .

“Rage kudaden da ake kashewa domin yin tsimin da zai ingiza tattalin arziki gaba, akwai kasashen da suka samu nasara a sakamakon bin wannan tsari, akwai kuma wadanda suka gaza, amma ni a lokaci na tare da hadin kan ku za mu yi aiki tare domin tabbatar da ganin mun kai ga samun nasara”

A jawaban su daban daban, manyan masu masana`antu da shugabannin bankuna da sauran `yan kasuwa sun yi wa shugaban na Najeriya alkawarin cewa za su yi bakin kokarin su wajen baiwa gwamantin sa gudumowar da zai kai ga samun nasarar shirye shiryen cigaban tattalin arzikin kasar.(Garba Abdullahi Bagwai)