logo

HAUSA

Maganin yaki da Malaria na Sin zai yi matukar tallafawa Uganda

2024-04-07 16:13:56 CMG Hausa

Ministar ma’aikatar lafiya a kasar Uganda Jane Ruth Aceng, ta ce magungunan yaki da cutar zazzabin cizon sauro ko Malaria da kasar Sin ta tallafawa Uganda da su, wadanda kimar su ta kai dalar Amurka miliyan 1.1, za su yi matukar taimakawa kasar wajen yaki da annobar ciwon.

Ministar wadda ta bayyana godiya ga kasar Sin, ta ce a bara, Uganda ta sha fama da bazuwar ciwon na Malaria, wanda ya yadu zuwa kusan sama da rabin gundumomin kasar.

Uwar gida Aceng, ta bayyana hakan ne a ranar Juma’a, bayan karbar magungunan, daga jakadan Sin a Uganda Zhang Lizhong, a babbar ma’ajiyar kayayyakin kiwon lafiya dake Kajjansi, gundumar tsakiyar Wakiso ta tsakiyar kasar. (Saminu Alhassan)