logo

HAUSA

Shugaban mulkin sojan Nijar ya rusa majalisun yankuna, birane, da gundumomin kasar

2024-04-05 15:30:46 CMG Hausa

 

Abdourahamane Tchiani, shugaban majalisar tsaron kasar Nijar CNSP, ya ba da umarni a jiya Alhamis, wanda ya rusa majalisun yankuna, birane da gundumomin kasar, kamar yadda kamfani dillancin labarai na Xinhua ya ruwaito daga majiya mai tushe.

Daga nan ne Tchiani ya rattaba hannu kan wata doka ta nada wakilai masu gudanar da aiki, bisa shawarar minista mai kula da harkokin cikin gida, don gudanar da kananan hukumomin yankunan karkara, da birane, da gundumomi. (Yahaya)