logo

HAUSA

An gudanar da zaman sakatarori na taron kiyaye tsaro na SCO karo na 19

2024-04-05 16:41:37 CMG Hausa

An gudanar da zaman sakatarori na taron kiyaye tsaro na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO karo na 19 a birnin Astana dake kasar Kazakhstan a ranar 3 ga wannan wata, inda shugaban ma’aikatar tsaron lafiyar al’ummar kasar Sin Wang Xiaohong ya halarci zaman tare da yin jawabi.

A cikin jawabinsa, Wang Xiaohong ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da membobin kungiyar SCO wajen aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashe membobin kungiyar suka cimma tare, da bin kiran kiyaye tsaron duniya, da yada tunanin Shanghai, da raya kungiyar SCO, da nuna goyon baya ga juna da yin hadin gwiwa, da kin amincewa da tsoma baki da sauran kasashe suka yi, da neman samun bunkasuwa tare, da mai da hankali ga aikin yaki da ta’addanci, da zurfafa hadin gwiwarsu, da raya kimiyya da fasaha, da tinkarar sabon salon laifuffuka, da yin imani da hadin gwiwa da juna a dukkan fannoni, ta haka kungiyar SCO za ta kara taka rawa gani kan kiyaye tsaron kasa da kasa da yankuna, da tinkarar kalubale a fannin kiyaye tsaro, da kuma tabbatar da zaman lafiya a duniya baki daya. (Zainab Zhang)