logo

HAUSA

An Bukaci Kasashen Afirka Da Su Yi Koyi Da Nasarorin Kasar Sin Na Kawar Da Talauci

2024-04-05 16:58:55 CMG Hausa

An bukaci kasar Habasha da sauran kasashen Afirka da su yi koyi da nasarorin da kasar Sin ta samu wajen kawar da talauci, a matsayin kokarinsu na raya tattalin arziki da fitar da miliyoyin mutane daga kangin talauci.

Jami'ai da kwararru na kasar Habasha sun jaddada cewa, tsarin musamman na kawar da talauci na kasar Sin ya taimaka wajen fitar da jama'a daga kangin talauci, ta hanyar aiwatar da cikakkun shirye-shiryen raya zamantakewar al'umma da tattalin arziki, da kuma raya albarkatun kasa ta hanyar da ta dace da kiyaye muhalli.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a kwanan baya, jam'iyyar Prosperity Party mai mulkin kasar Habasha ta bayyana cewa, a halin yanzu, tawagar manyan jami'an jam'iyyar tana ziyarar aiki a kasar Sin, inda suka duba tsarin kasar Sin na kawar da talauci da kuma kwarewa baki daya.

Sanarwar ta ruwaito Addisu Arega, jami’in jam'iyyar Prosperity Party mai kula da hulda da jama'a da na kasa da kasa, bayan da ya ga ayyukan ci gaba a kasar Sin, na cewa, nasarorin da gwamnatin kasar Sin ta samu wajen rage talauci sun zama abin koyi ga Habasha.

Tawagar ta jaddada cikin sanarwar cewa, nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin kawar da talauci, da raya muhalli wajen kawo sauyi a yankunan hamada, ta hanyar daidaita al'umma, da kuma nasarorin da aka samu wajen tabbatar da hadin kan kasa, don gaggauta samun bunkasuwa, na daga cikin fannonin da kasar Habasha za ta iya daukar darasi daga cikinsu. (Yahaya)