logo

HAUSA

Shugaban tarayyar Najeriya ya sanya hannu kan dokar rancen kudin karatu ga daliban manyan makarantun kasar

2024-04-04 16:31:23 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannun kan kudurin dokar samar da bashi ga daliban manyan makarantun kasar domin gudanar da karatun su.

Shugaban ya sanya hannun ne ranar larabar 3 ga wata a fadarsa dake Abuja, dokar wadda aka yi wa kwaskarima za ta bayar da damar kafa asusun lura da harkokin ba da rance ga dalibai na kasa.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Ministoci da ‘yan majalissa da kuma manyan masu ruwa da tsaki a harkar ilimin kasar suna daga cikin wadanda suka sheda bikin sanya hannun.

An dai kai ruwa rana kafin wannan lokaci da aka sanyawa dokar hannu, bayan da majalissun dokokin kasar suka kammala gyara kudurin dokar zurfafa ilimi ta 2024.

A lokacin da yake jawabi kafin sanya hannun kan dokar, shugaban na tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce, wannan sabuwar doka na daya daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa da za su bunkasa sha’awar matasa wajen neman ilimi a kasar.

Shugaban ya ce, ilimi shi ne makamin yakar talauci, kuma mun kuduri aniyar baiwa ilimi kulawar da ta kamata tare da bunkasa sauran fannonin fasahohin hannu daban daban domin ganin cewa babu ko da mutum guda a kasar da za a bari cikin jahilci don samun rayuwa ingantaciyya.

“Ina mika godiya ta ga ‘yan majalissar dokoki ta kasa saboda hanzartar zartar da wannan kudurin doka, ta hanyar la’akari da daliban Najeriya, mun kasance a wanann matsayi ne saboda dukkannin mu nan mun samu ilimi kuma mu ma mun samu taimako a wancan lokaci, a baya za ka ga yara da yawa ana korar su daga kwalejoji, yanzu dama ta samu ga kowanne yaro, ya mika bukatar sa ta neman rancen kudin karatu muddin dai mutun dan Najeriya ne.” (Garba Abdullahi Bagwai)